1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na makokin tuni da harin nukliya kan Nagasaki

Gazali Abdou TasawaAugust 9, 2015

Makamin kare dangi na nukliya da Amirka ta harba a birnin Nagasaki na Japan ran 09.08.1945 ya halaka mutane sama da dubu 74

https://p.dw.com/p/1GCIU
Japan 70. Jahrestag Atombombenabwurf Zweiter Weltkrieg in Nagasaki - Denkmal
Hoto: Reuters/Kyodo

A kasar Japan al'ummar birnin Nagasaki sun yi tsit na tsawon minti daya a wannan Lahadi domin tunawa da ranar zagayowar cikan shekaru 70 da birnin ya fuskanci harin makamin nukliya, daga kasar Amirka da karfe 11 da mintoci biyu na ran 09.08.1945 a lokacin yakin duniya na biyu.

Mutane kimanin 74000 ne suka halaka, kuma sama da kashi 80 daga cikin dari na gidajen birnin na Nagasaki suka rushe. Harin makamin kare dangin da birnin ya fuskanta a wancan lokaci, ya farau ne kwanaki uku bayan da dama kasar Amirkar ta hari birnin Hiroshima na kasar ta Japan da irin wannan makami, inda mutane kimanin 140,000 suka halaka.

Biyo bayan wadannan hare-haren makaman kare dangin ne dai, kasar ta Japan ta yi saranda ranar 15.08.1945 wanda haka ya kawo karshen yakin duniya na biyu. Taron makokin tunawa da wannan rana da ya gudana a yau Lahdi, ya samu halartar wakilai daga kasashe 75 na duniya.