1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Abdullahi Tanko Bala LMJ
July 2, 2018

Rashin taka rawar a zo a gani da kasashen Afirka suka yi a gasar kwallon kafa na duniya ta bana da bude kamfanin Volkswagen a Ruwanda ya dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/30hNo
Nigerianische Fußball-Nationalmannschaft
Kasashen Afirka sun gaza kai gacci a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta banaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Jaridar die Tageszeitung ta fara da waiwayen baya inda ta tabo rawar da nahiyar Afirka ta taka a gasar kwallon kafa ta duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 wato  U17. Jaridar ta ce sau uku Najeriya na daukar wannan kambu, sai dai ta ce abin bakin ciki da takaici ba a taba samun wata kungiya ta Afirka da ta taba kai wa zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya ba. Matsala guda da 'yan wasan kwallon kafa na Afirka ya kamata su yi la'akari da ita a koda yaushe ita ce aiki da lissafi. A 2010 a Afirka ta kudu haka aka fidda Najeriya ba tare da ta kai ko ina ba.

Karawar da Najeriya ta yi da Kwuroshiya a gasar cin kofin duniyar ta bana ta kasance mai wahala, inda a bisa kuskure ta zurawa kanta kwallo a raga. Duk da cewa sun yi kokari a wasan da suka yi da Iceland da ci biyu da nema a cewar jaridar, sai bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ne Viktor Moses da Ahmed Musa suka fahimci bukatar kara kaimi. A karshe jaridar ta ce manazarta na hasashen habakar kwallon kafa a Afirka ba tare da kai wa gacci ba, sai dai ta ce akwai kyakkyawan fata kamar yadda mai horar da 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya nuna kwarin gwiwar cewa kungiyar na iya taka sa'a a shekara ta 2022.

A waje guda kuma Jaridar ta die tageszeitzung a sharhinta mai taken "Afirka na bunkasa hatta a fannin sufuri." Jaridar ta ce Ruwanda ta shiga sahun gaba da samar da kamfanin kera motocin Volkswagen a cikin kasar. Ta ce an bude sabon babi na habakar tattalin arziki yayin da Shugaba Paul Kagame ya zuba jarin dala miliyan 16 a Volkswagen domin kafa kamfanin a cikin kasar. Ruwanda na son fadada daga fannin noma zuwa sufuri. Kamfanin wanda shi ne na farko a cikin kasar zai rika hada motocin Volkswagen samfurin Polo kuma matakin zai taimaka wajen inganta sufuri da ma samar da ababen hawa ga kasashe makwabta kamar Yuganda da Kenya da kuma Tanzaniya.