1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jarrabawar WAEC ta nuna koma bayan ilimi a Najeriya

December 20, 2013

Sakamakon jarrabawar kammala sakandare da WAEC ta shirya a wannan shekara ta nuna karuwar faduwar jarrabawa a tsakanin daliban Najeriya.

https://p.dw.com/p/1AeL9
Hoto: DW/A. Stahl

Tabarbarewaqr ilimi a makarantun Najeriyar dai ba sabon abu ne, domin kuwa batun satar jarrabawa ko baiwa dalibai amsa a kaikaice wajen jarrabawar na neman zama tsohon yayi, inda kiri-kiri ake dauko sojojin haya don su rubutawa dalibai jarrabawar kammala karatu, abinda kwararru ke danganata shi da rubdugun da ake fuskanta a wannan sashi.

Sakamakon jarrabawar na wannan shekarar dai ya nuna mummunan koma bayan da aka fuskanta da yafi na kowace shekara muni, musamman idan aka kwatanta da nasarar da daliban da suka kamala sakandaren suka samu a shekaru uku da suka gabata a kasar, domin kuwa alkaluman da hukumar kula da shirya jarrbawar sakandaren ta WAEC ta fitar, suna nuna cewa kasha 40.46 ne suka samu lashe darussa shida, yayin da kashi 54.48 suka samu lashe darussa biyar. To shin me ke haifar da yawaitar faduwar jarrabawa ne da a kullum ya zama gwamma bara da bana? Alhaji Garaba Jiji Gadam, kwararre ne a kan harkar ilimin sakandare, kuma tsohon malamin makaranta a Najeriyar.

‘'Yawanci dai matsalar ta malamai ce, domin kaje makarantun sakandare mana ka gani, domin an kashe makarantun samar da malamn makaranta a yankin arewacin Najeriya , domin da can akwai wadannan makarantu sannan akwai kuma na sakandire. A lokacin zaka zo kayi grade 3 ka yi 2 kai har ka samu 1 ma, don haka duk inda aka kai ka zaka iya koyarwa mai kyau''.

Abinda yafi daga hankali a sakamakon jarrabawar na wannan shekara shine yadda aka samu yawaitar daliban da suka samu nasara a darassu biyu kacal, wanda ba yadda zasu iya ci gaba da karatun nasu, domin kuwa yawansu ya kai kashi 86, watau dalibai 256,500 daga cikin adadin dalibai 308,217 da suka yi rajistar.

Afrika Schulkinder
Yan makaranta tushen ci gaban ko wace kasaHoto: SEYLLOU/AFP/Getty Images

Zargin da akan yi a kan tabarbarewar daukacin tsarin ilimin boko tun daga firamare har zuwa jami'a, abinda ke ci gaba da jefa yanayin ilimin bokon kasar cikin mawuyacin hali kara sukurkucewa a kasar. Wannan ya sanya kwararre a wannan fanni irin su Dr. Hussaini Tukur da bayyana illar da wannan ke da ita ga makomar Najeriyar.

‘'Wannan abu ba karamar illa bane, domin duk tasuniyoyi da muke na zamu samu ci gaba a duniya zasu zama almara, saboda ba kokarin da muke mu ga mun cimma wannan ta irin wannan harkokin''.

Dukkanin kokarin da na yi don jin ta bakin hukumar wace da ke shirya jarrabawa kammala sakandare abin yaci tura, duk da safa da marwan da suka sanyani a ofsihinsu da ke Abuja.

Entwicklungshilfe Afrika
Daliban yau, shugabannin gobeHoto: picture-alliance/dpa

A yayin da ake ci gaba da nuna damuwa akan tabarbarewar ilimin Najeriyar inda daga makarantun gwamnatin zuwa na masu zaman kansu sannu a hankali ana zubargada ne kawai, wanda abin yafi shafa shine talaka a yanzu, don masu kudi tura ‘ya'ansu kasashen waje suke yi, sai dai shin a wace kasa ne zasu dawo su rayu har su yi aiki in sun kammala karatu a kasashe waje?

Mawallafi: Uwais Idris Abubakar
Edita: Umaru Aliyu