1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Merkel a majalisa kan NATO da Rasha

Umaru Aliyu/ GATJuly 7, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Alhamis ta yi wa majalisar dokoki ta Bundestag bayani a game da manufofin gwamnatinta kan batun tsaro da kuma dangantaka tsakanin Kungiyar NATO da Rasha.

https://p.dw.com/p/1JLN5
Deutschland Angela Merkel Regierungserklärung in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

A jawabinta gaban wakilan majalisar ta Bundestag a Berlin, shugabar gamnatin ta Jamus ta ce taron koli na kungiyar tsaron ta NATO, zai aika wa da Rasha sakonni ne guda biyu. Sakon farko shi ne, kungiyar ta tsaro za ta nunar wa Rasha a fili cewar za ta tsaya sosai wajen taimaka wa kasashen yankin Gabashin Turai, domin kare su daga duk wasu hare-hare daga Rashan, ko da wadannan hare-hare kuwa sun shafi amfani da na'urorin sadarwa ne na zamani.

Merkel ta ce saboda haka ne ya zama wajibi kungiyar NATO din ta kara karfin kasancewarta a kasashen yankin Balkan da Poland, ta fuskar makamai da soja. Sai dai ta kara da cewar tana sane da cewar zaman lafiya mai dorewa a Turai ba zai samu ba sai tare da hadin kan Rasha.

Shirin NATO na kara yawan rokokin kariya a Gabashin Turai ba mataki ne na adawa da Rashar ba, amma sai domin kara karfin tsaro, bisa lura da cigaba da shirin Iran na daura wa kanta damarar rokokin kai hare-hare. Shugabar gwamnatin ta yi magana a game da sanyin dangantaka tsakanin kasashen NATO da Rasha, inda ta ce shugabanni a Mosko su suke da alhakin hakan.

Berlin Kanzlerin Merkel in Rede vor dem Bundestag
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

"Idan kasa ta yi watsi da dokokin da suka shafi hana keta haddin iyakokin makwabtanta, to kuwa ba abin mamaki ba ne hakan ya yi jagora ga zubewar mutunci da raguwar amince wa juna. Irin wannan mataki ma shi ya kawo raunanar matsayin kasashe kawayenmu a Gabashin Turai, abin da a daya hannun, ya sanya suke bukatar tabbacin samun kariya daga kungiyar ta hadin kan tsaro. Yakin basasa a Siriya da rushewar kasashe kamar Libya da Iraki, sun sanya an samu karuwar kungiyoyi na 'yan ta'adda, ga kuma yaduwar kungiyoyin da ke aikin safarar mutane, da ke amfani da mummunan halin da dimbin 'yan gudun hijira suke ciki domin cin ribarsu."

Shugabar gwamnatin ta shaida wa majalisar a Berlin cewar tana goyon bayan daukar karin kasashen yankin Balkan a NATO. Ta ce kungiyar ba za ta rufe kofofinta ga kasashe masu neman kasancewa wakilai a cikinta ba, ko da shi ke ba ta ambaci sunan wasu kasashe musamman ba. Duk da hakan an yi imanin kasashe kamar Montenegro da Jojiya da Ukraine nan gaba kadan za a fara tattaunawa da su game da neman shiga kungiyar. Dangane da haka, shugaban gwamnati, Angela Merkel ta ce:

"Burin al'amarin dai shi ne bai wa kungiyar NATO damar kara karfin kasancewarta a kasashen yankin Balkan da Poland, karkashin taken: gani ga wane, ya isa wane tsoron Allah. Yin hakan ya zama wajibi saboda mun lura da cewar gaggauta kai sojoji wadannan yankuna da zaran wani abu ya samu, ba zai wadatar ba, abin da ke da muhimmanci shi ne mu kasance a can yadda hakan zai hana taba kasashen yankin".

Berlin Regierungserklärung Angela Merkel im Bundestag
Hoto: Getty Images/AFP/A. Berry

Shi ma a jawabinsa gaban majalisar, kakakin wakilan jam'iyar SPD Thomas Oppermann ya goyi bayan kungiyar ta NATO, inda ya ce mamayewar da Rasha ta yi wa yankin Kirimiya na Ukraine ya kawo barazana ga zaman lafiyar Turai. Amma a nata bangaren, kakakin jam'iyyar Linke ta masu neman canji, ta yi Allah wadai ne da atisayen baya-bayan nan da NATO ta yi a Poland, inda ta ce wannan ba komai ba ne illa shirin yaki, kuma tare da taimakon Jamus.

Sauran al'amuran da Merkel ta tabo a jawabinta gaban majalisar dokokin ta Bundestag, wadanda kuma ta ce sun zama kalubale ga kungiyar, sun hada har da yakin basasa a Siriya da rushewar kasashen Irak da Libya wadanda suka haddasa karuwar barazana ga tsaro da zaman lafiyar Turai.