1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jibuti: Kimanin 'yan gudun hijira 30 sun halaka

Yusuf Bala Nayaya
January 30, 2019

Akalla 'yan gudun hijira 28 ne suka nitse a teku bayan da jiragen ruwan da ke dauke da su guda biyu suka kife ba nisa da gabar teku a Jibuti.

https://p.dw.com/p/3CRQl
Dschibuti Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/International Organization for Migration

Mai magana da yawun hukumar 'yan gudun hijira ta IOM Joel Millman, ya fada wa kamfanin dillancin labaran na Jamus cewa suna da tabbaci na samun gawarwaki 28 haka kuma an samu mutane biyu a raye. Ya kara da cewa suna tsammanin cewa adadin wadanda suka mutu za su haure haka.

Fiye da 'yan gudun hijira 130 mafi yawa 'yan Habasha da suka nufi Yemen ke cikin jiragen lokacin da suka kife a kusa da Godoria yankin da ke Arewa maso Gabashin karamar kasar ta Jibuti da ke yankin kahon Afirka a ranar Talata, kamar yadda hukumar ta IOM ta samu bayanai.

Kasar ta Jibuti dai ta kasance hanya da 'yan gudun hijira dubbai ke amfani da ita a kokari na shiga kasashen Larabawa a cewar hukumar da ke kula da 'yan gudun hijirar kasa da kasar ta IOM.