1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen kasa a Jamus zasu koma aiki

Yusuf BalaNovember 7, 2014

Kungiyar direbobin jiragen kasa da suka shiga yajin aiki tun daga ranar Laraba a Jamus, ta bayyana cewa ta takaita yajin aikin da take yi zuwa Asabar.

https://p.dw.com/p/1DjAT
Lokführerstreik - Frankfurt
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan yajin aiki da aka shirya tun da fari za a kammala a ranar Litinin, na zuwa ne adaidai lokacin da ake shiga ruguntsumin bikin tunawa da ranar faduwar katangar Berlin karo na 25 a karshen mako.

Claus Weselsky da ke zama jagoran kungiyar direbobin jiragen kasan na Deutsche Bahn, ya bayyana cewa za a kawo karshen yajin aikin ne a ranar Asabar da misalin karfe shida na yammaci, hakan kuwa na zuwa ne bayan da kotu ta yi watsi da karar da kamfanin dake lura da harkokin safarar jiragen kasar na Jamus Deutsche Bahn na cewa yajin aikin da direbobin suka shiga baya bisa ka'ida.

Wannan yajin aikin dai, ya tsaida zirga-zirgar jama'a da safarar kayayyaki a wannan kasa da ke da mutane miliyan tamanin da biyu, lamarin da ya kawo nakasu ga zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki.