1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiran sakamakon zaɓen kundin tsarin mulki a Masar

December 23, 2012

'Yan adawar Masar za su shigar da ƙara kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen saban kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/178JM
Egyptian election workers empty a ballot box for counting at the end of the second round of a referendum on a disputed constitution drafted by Islamist supporters of president Mohammed Morsi at a polling station in Giza, Egypt, Saturday, Dec. 22, 2012. Egypt's Islamist-backed constitution headed toward likely approval in a final round of voting on Saturday, but the deep divisions it has opened up threaten to fuel continued turmoil. (Foto:Nasser Nasser/AP/dapd)
Kidayar uri'un zaɓe a MasarHoto: AP

Jam'iyun adawa a Masar, sun yi wasti da sakamakon zaɓen raba gardama game da saban kundin tsarin mulki da aka kammalla jiya.A hukunce a wannan Litinin ake sa ran baiyana sakamakon zaɓen,to saidai 'yan uwa musulmi tare da sauran ƙungiyoyin dake goya musu baya, sun ce sun samu gagaramin rijnaye tare da kashi 64 cikin ɗari na mutanen da suka amince da kundin.

'yan adawar sun ce, za su shigar da ƙara kotu domin ƙalubalantar wannan sakamako, da su kace ya na cike da maguɗi.Masu adawa da saban kundin na zargin shugaba Mohammad Mursi da ƙadamar da shari'ar musulunci a cikinsa, da kuma tauye 'yancin jama'a.

A yayin da yake tsokaci game da zaɓen na Masar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira ga hukumomin Alƙahira su kasance masu adalci a duk cikin al'amura.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu