1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin saman kasar Turkiya ya yi hadari a Kirgistan

Salissou Boukari
January 16, 2017

Akalla mutane 32 ne suka mutu cikinsu yara kanana shida sakamakon hadarin wani jirgin sama na daukan kaya na kasar Turkiya wanda ya fadi bisa gidaje kusa da filin jiragen sama na Bichkek da ke kasar Kirgistan.

https://p.dw.com/p/2VqRm
Kirgistan Flugzeugabsturz
Baraguzzan jirgin saman da ya fadi bisa gidaje a kasar KirgistanHoto: Reuters/V. Pirogov

Bayan dai wani adadi na farko da ya sanar da mutuwar mutane 15, zuwa 20 a ofishin ministan kiwon lafiya na kasar ta Kirgistan ya sanar da wannan sabon adadi na mutane 32 cikinsu har da matukan jirgin guda hudu, inda wata majiya ta asibitoci ta tabbatar da kasancewar yara kanana guda shida daga cikin wadand suka mutu.

Jirgin dai ya taso ne daga birnin Hong-Kong na kasar Chaina, kuma ya fadi ne a kusa da filin jirgin saman Manas na jihar Bichkek sakamakon rishin kyawon yanayi a cewar Moukhammed Svarov, wani jami'in ma'aikatar agaji ta kasar Kirgistan.