1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Kerry da wani dan majalisar dattijai sun gana da shugaba Assad

December 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuWw

Wasu fitattun ´yan majalisar dattawan Amirka ciki har da tsohon dan takarar shugaban kasa karkahin tutar Democrats John Kerry sun gana da shugaban Syria Bashar Al-Assad. Ofishin jakadancin Amirka ya ce mista Kerry da Chris Dodd wadanda dukkan su membobin kwamitin dake kula da huldodin ketare na majalisar dattawan ne, sun tattauna da Assad a kan batutuwa da dama ciki har da hulda tsakanin Amirka da Syria da kuma wadanda suka shafi yankin GTT. Sinatocin su biyu sun kuma gana da ministan harkokin wajen Syria Walid al-Moallem, to amma sun ki su yi magana da manema labarai. ´Yan majalisar sun kai wannan ziyara a Damascus duk da sukar da gwamnati a Washington ta yi game da yin haka.