1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Kerry na rangadin aiki a Turkiyya

March 1, 2013

Amirka ta bukaci ganin ingantuwar dangantaka tsakanin Turkiyya kan Izra'ila, sakamakon furucin da firayiministan Turkiyya ya yi a taron MDD a Vienna.

https://p.dw.com/p/17p0h
: POLITICS)
Hoto: Reuters

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana rashin jin dadinsa da furucin firayiminstan Turkiyya na cewar ta'assar da gwamnatin Izra'ila ta ke yi daidai yake da kisan kare dangi. Kerry dake rangadinsa na farko a wata kasar Musulmi tun bayan hawansa wannan mukami, zai gana da shugabannin Turkiyyan, a wata tattaunawar da za ta mayar da hankali kan yakin basasar da ke gudana a kasar Siriya, da hadakar makamashi domin shawo kan matsalar ta'addanci. Sai dai furucin da firayiminstan Tayyip Erdogan yayi a taron MDD a birnin Vienna a wannan makon, wanda ya samu suka daga Izraela da fadar gwamnati ta white house da babban sakatare Ban Ki-moon, zai mamaye tattaunawar rangadin sakataren harkokin wajen Amurka a Turkiyya.Ya fada wa taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa Ahmet Davutoglu cewar, Izra'ila da Turkiyya abokan huldodin Amirka ne, dangane da haka ne take muradin ganin cewar an samu kyautuwar danganta tsakanin bangarorin biyu.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abukakar
Edita : Saleh Umar Saleh