1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya hada tawagar kampe

Ubale MusaJanuary 2, 2015

Ofishin shugaban Najeriya ya sanar da sunayen wadanda zasu jagoranci kampe da Jonathn zai fara na neman ci gaba da mulki

https://p.dw.com/p/1EEM5
Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014
Hoto: picture-alliance/AP

A wani abun dake zaman kama hanyar fara yakin neman zabe gadan- gadan ga shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan dake neman sake zama shugaban kasa bisa sabon wa'adi, ofishin shugaban kasar ya fitar da sunayen mutanen da zasu ja ragamar yakin neman zaben a cikin hanyar dake da alamun tsidau da kaya.

Na kan gaba a cikin jerin sarakunan yakin na Jonathan dai na zaman tsohon shugaban jam'iyyyar Col Ahmadu Ali mai ritaya dake da jan aikin saida shugaban cikin kasa a cikin halin rashin tsaro da ma barazanar rushewar tattalin arziki a kasar.

A yayin kuma da fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock ta kai ga nada masa wasu jerin mataimaka guda uku da suka hada da Barrister Kabiru Tanimu Turaki da zai tamaka masa daga arewa, sannan da Peter Obi dake zaman tsohon gwamnan jihar Anambra kuma zai taimaka masa daga sashen kudu maso gabashin kasar ta Najeriya.

Farfesa Tunde Adeniran ne dai ke zaman mataimaki na uku daga sashen kudu maso yamma da kuma zai jagoranci harkokin gudanarwar mulkin hedikwatar yakin neman zaben na tsawon wasu makonni shidan dake tafe.

Sauran 'ya'yan jam'iyyar da zasu taka rawa cikin jagorantar sake tabbatar da zaben na Jonathan dai na zaman Chief Tony Anenih dake zaman mai bada shawara na musamman kan yakin da kuma Senata Nenadi Usman dake zaman daraktar bangaren kudi, sannan da Modibbo Aliyu Umar da zai kula da harkokin mulki.

Symbolbild Entführungen von Frauen und Mädchen in Nigeria
Masu zanga-zangar neman dawo da 'yan matan ChibokHoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

Farfesa Jerry Gana ne dai zai kula da tara magoya baya ga shugaban, a yayin kuma da aka nada Femi Fani Kayode domin aikin kula da harkokin jaridu. Duk da cewar dai da damansu sun yi fice cikin harkoki na siyasar kasar ta Najeriya ana kallon sabbabin nadin a matsayin ko dai wadanda tsufa ya tarar, ko kuma jininsu ya fara sauya launi zuwa baki a siyasar kasar a halin yanzu.

Ko bayan jan aikin tabbatar da hallarcin takarar dai, limaman zarcewar na Jonatahn na da jan aikin gamsar da yan kasar hujjar sake zaben shugaban da har yanzu yake damarar yakar hanci, ko bayan gaza shawo kan batun rashin tsaro cikin kasar. To sai dai kuma a fadar farfesa Rufa'i Alkali dake baiwa shugaba Jonathan shawara kan batun siyasa da kuma ya sanar da sabbabin sunayen dai, cancanta da kwarewa dama farin jini na sannaya na zaman al'amuran da aka maida hankali kansu wajen zabn mutanen.

"Yawancin mutanen in ka duba zaka tarar mutane ne sun san gwamnati, sun san jama'a. Shi yasa aka zabo su kuma aka tabbatar an dauko kowa daga lungu-lungu da sako-sako na Tarrayar Najeriya, kuma duka duka baifi kwanaki 40 bane da wannan zabe, ka ga kuma ai lokaci ya kure,

Hakuri da rashin son samu ko kuma hakuri da shiri na runguma ga kaddara, dai a karon farko 'ya'yan PDP na fuskantar adawa mafi karfi da ma farin jinin da babu irinsa cikin tarihi na sake dawowar demokaradiya cikin kasar a halin yanzu".

Nigeria - nominierter Präsidentschaftskandidat Muhammadu Buhari
Dan takarar jam'iyar adawa ta APC, Janar Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/P. Ekpei

Su kansu masu adawar kasar ta Najeriya dai sunce wai girman sunayen na Jonathan bai isa hanasu tunkarar kalubalen dake tafe da kuma ke shirin tantancewa tsakanin 60 da 16 na shekarun mulkin PDP a kasar a fadar Eng. Buba Galadima dake zaman jigo a cikin jam'iyyar APC ta adawa.

Abun jira a gani dai na zaman wanda zai kai ga nasara a karon batta da ya dauki lokaci yana ban tsoro cikin kasar da kuma ke iya bude sabon babi cikin fagen siyasar Najeriya.◄