1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyayi da alhinin rasuwar Chinua Achebe

March 22, 2013

Marubucin wanda ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, shi ne marubucin da ya wallafa littafin adabin Afirka da ya fi samun karbuwa a duniya wato Things Fall Apart.

https://p.dw.com/p/182sr
Nigerian author Chinua Achebe gestures during a news conference held during the Frankfurt bookfair in this October 12, 2002 file photo. Achebe, widely seen as a grandfather of modern African literature, has died at the age of 82, publisher Penguin said on March 22, 2013. REUTERS/Ralph Orlowski/Files (SOCIETY HEADSHOT OBITUARY)
Hoto: Reuters

Shahararen marubucin adabin nan na nahiyar Afirka wato Chinua Achebe dan Najeriya ya mutu a daren Alhamis zuwa Juma'a a birnin Boston na kasar Amurka. Ba a dai bayyana cutar da ta yi sanadinsa ba, amma dai na kusa da danginsa sun baiyana cewa Achebe ya shafe tsawon lokaci ya na fama da rashin lafiya. Chinua Achebe wanda ya shafe shekaru 82 a duniya, shi ne marubucin da ya wallafi littafin adabin Afirka da ya fi samun karbuwa a duniya. Wannan littafin mai suna Things Fall Apart an fassara shi cikin harsuna 50 tare da sayar da miliyon 12 daga cikin wadanda aka buga.

An haifi Chinua Achebe a garin Ogidi da ke cikin jihar Anambra ta Tarayyar Najeriya a shekarar 1930. Tun ya na dalibi ya fara rubuce rubuce a rayuwarsa. Amma kuma littafin da ya fi haddasa kace nace shi ne wanda ya shafi rayuwarsa da kuma ra'ayinsa kan yakin Biafra da ya rubuta a baya-bayan nan.

Bayan rasuwar shahararren marubucin nan na adabi kuma tsohon danjarida mai fafitika, wato Chinua Achebe, marubata a ciki da wajan Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu da nuna alhini ga wannan rashin .

Ko za a iya cewa wannan rasuwa ta marubucin gagarumin rashi ne a duniyar marubuta? Tambayar kenan da Yusuf Bala ya yi wa Farfesa Ismail Bala malami a sashen nazarin harshen Ingilishi na jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya, a cikin hirar da muka yi muku tanadin sautinta a kasa.

Mawallafa: Mouhamadou Awal / Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal