1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabore ne sabon shugaban Burkina Faso

Ahmed SalisuDecember 1, 2015

Hukumar zaben Burkina Faso ta bayyana Roch Marc Christian Kabore a mastayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar.

https://p.dw.com/p/1HF7J
Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Roch Marc Christian Kabore
Hoto: DW/K. Gänsler

Mr. Kabore dai ya samu kashi 53.4 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da babban mai hammaya da shi Zephirin Diabre ya samu kashi 29.3, batun da ke nuna cewar ba sai an yi zagaye na biyu a zaben ba. Tuni ma dai Mr. Diabre ya taya abokin takararsa murar lashe zaben.

Da ya ke jawabi gaban dubban magoya bayansa, Roch Marc Christian Kabore ya ce lokaci ya yi da za su dukufa wajen ganin fara aiki domin sake gina kasar domin amfanar al'ummar Burkina Faso. Al'ummar kasar kimanin miliyan 18 dai yanzu haka na fata na ganin sauyi bayan da a baya ta sha fama da tsoma bakin sojin wajen tafiyar da ita da kuma mulki irin na mahadi ka ture.