1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Samar da ilimi ga matan karkara

June 21, 2017

Wata gidauniya a jihar Kadunan Najeriya ta dauki nauyin karantar da matan aure na karkara karatu boko da na arabiya a wani yunkuri na yaki da jahilci a kauyukan da ke wannan jiha.

https://p.dw.com/p/2f6sX
ScreenshotsDW Sendung eco@africa
Hoto: DW

Yunkurinta na ganin matan aure da ke yankunan karkara da ma na birane na samun ilimin boko da na addini ne ya sanya ita wannan gidauniya mai suna Ar-Ridah Foundation fara wannan gagarimin shiri inda ta bude cibiyoyi da yawansu suka kai 17 a jihar ta Kaduna kuma yanzu haka wannan shiri tuni ya dauki dalibai kimanin 3,500.

Rabi Salisu Ibrahim da ke jagorantar wannan gidauniya ta ce saboda su habaka ililimin mata duba da irin gudumawar da suke bayarwa a rayuwar yau da kullum shi ne ya sanyasu ganin dacewar bijiro da wannan shiri na ilimantarv da matan. Daga fara wannan shiri kawo yanzu dai an yaye daliban da yawansu ya kai kimanin 700.

Baya ga ilimantar da matan, har wa yau gidauniyar na kuma horar da wadannan mata sana'o'i daban-daban da nufin basu damar dogaro da kansu bayan kammala daukar horon. Tuni dai wadanda suka ci moriyar wannan shiri irinsu Fatima Aliyu da ke zaune a Hayin Rigasa suka nuna jin dadinsu dangane da wannan talalfi da suka samu domin a cewarta yanzu kam za su iya yin karatu da rubutu kamar yadda ya dace.