1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa majalisar sasantawa a Afganistan.

September 4, 2010

Shugaba Hamid Karzai zai kafa komitin sasanatawa da 'yan Taliban.

https://p.dw.com/p/P4LA
Shugaba Hamid KarsaiHoto: AP

A wannan Asabar ce Shugaba Hamid Karzai na ƙasar Afghanistan ya yi shelar kafa majalisar sasantawa da ƙungiyar Taliban, wadda ke ta da ƙayar baya tun bayan hambarar da ita shekaru tara da suka gabata. Ofishin Shugaba Karzai ya sanar da cewar, kafa majalisar samar da zaman lafiyar, wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin daidaita lamura a ƙasar. A watan Yuni ne dai majalisar dokokin Afghanistan ta " Jirga " ta amince da kafa kwamitin sulhun, a yayin wani taron da ya sami halartar shugabannin siyasa da na addini da kuma na ƙabilu daga sassa daban-daban na ƙasar.

Mambobin majalisar sasantawar za su ƙunshi dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa, kama daga masu faɗa a ji ya zuwa shugabannin ƙungiyoyi da kuma mata. Dama an yi zaton Shugaba Karzai zai sanar da sunayen mambobin majalisar ne tun bayan wata ganawar da ya yi tare da tsohon jagorar ƙungiyar Mujahideen Burhanuddeen Rabbani, da kuma Abdul Rasul Sayyaf, da kuma wasu jami'ai inda suka tattauna da wakilan da za su kasance a cikin kwamitin. Bayan bukukuwan Sallar Idi - a makon nan da ke tafe ne idan Allah ya kai mu shugaban zai bayyana jerin sunayen mambobin majalisar sasantawar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas