1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana muzgunawa rayuwar mata a duniya

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 7, 2015

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki al'ummomin kasa da kasa da abin da ta kira cin zarafin mata da yara mata.

https://p.dw.com/p/1En3P
Selmin Caliskan, sakatare janar ta kungiyar Amnesty International a Jamus
Selmin Caliskan, sakatare janar ta kungiyar Amnesty International a JamusHoto: DW/B. Marx

Janar sakatare ta kungiyar a nan Jamus Selmin Caliskan ce ta bayyana hakan yayin hirar da ta yi da wata jarida da ke fitowa duk rana a Jamus, inda ta ce lamarin ya kazanta a shekarar da ta gabata duba da yadda aka samu karuwar tashe-tashen hankula nan da can. Ta kara da cewa abin damuwa ne yadda a ko yaushe ake samun karuwar mata da yara mata da ke shiga halin ni 'yasu yayin yaki. Caliskan ta ce ana cin zarafin mata yayin yaki ta hanyar yi musu fyade da muzguna musu inda ta ce ya zamo wajibi a yi maganin wannan matsala domin ganin an inganta rayuwar matan.