1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen dimokradiyya a Najeriya

May 29, 2014

Al'ummar Najeriyar dai na bukin shekaru 15 na dimokradiyyar ce, cikin rigingimu na Boko Haram da matsalolin rayuwa da suka dabaibaye kasar, kuma babu mafita.

https://p.dw.com/p/1C8yc
Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan in Brüssels
Hoto: picture-alliance/dpa

Shekaru goma sha biyar kenan a jere da sake samun kafuwar mulkin dimokradiyya a Najeriyar, shekarun da suka kasance cike da barazana, kalubale da ma takadamma a fanonin dab an na rayuwar gwamnatocin kasar da suka gabata. Ga gwamnatin da ke mulki yanzu a Najeriayar wace ke bikin zagayowar shekaru uku da hawa kan mulkin ta kasance wace ke fuskantar matsalar kaluballen rashin tsaro da yafi ta'azarra fiye da na sauran lokutan da suka gabata.

A yanzu da Najeriyar da al'ummarta ke murnar wannan rana shin ya tafiyar ta kasance ga kasar ne, ko za'a ce kwalliya ta biya kudin sabulu ga dimmukurdiyyar Najeriya? Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja.

"A dunkule za'a iya cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba domin a 'yan shekaru 15 da aka yi a karkashin tutar jam'iyyar PDP a tsakiya za'a iya cewa Najeriya ta dan samu wasu kwarya-kwaryar ci gaba, sannan idan aka duba ta daya bangaren watau na gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan abubuwan da suka wakana a shekaru uku yana mulki, in dai an bi ta bayanin jama'a ne da kuma zamantakewar al'umma a nan dinma dai za'a ce kwalliya bata biya kudin sabulu ba".

Nigeria Protest Boko Haram Entführung 26.5.2014
Gangamin bukatar sako'yan ChibokHoto: picture-alliance/AP Photo

To sai dai ga gwamnati Najeriyar a karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan na mai ikirarin samun ci gaba a fanonin da dama duk kuwa da irin nasarorin da aka samu a kasar a cikin shekaru ku da tayi tana jan ragamar kasa. Amma ga Alha Isa Tafida Mafindi jigo a jamiyyar PDP na mai bayyana cewa samun dorewar dimokrdiyyar na tsawon shekaru 15 a jere abin a yi biki ne har ma da guda.

A yayin da ake ci gaba da tatata da ma muharawar shin Najeriyar mulkin dimukurdiyyar take yi ko kuwa na fara hula, rashin nuna gamsuwa da wannan tsari na dimokrdiyya da al'ummar Najeriya ke nunawa saboda gazawar tsarin wajen kaisu tudun na tsira na cike da hatsari.

Bikin na wannan rana da ke zama na karhse ga wannan gwamnati na cike da muhimmancin gaske, saboda yadda 'yan siyasa da ke ci gaba da tufka lissafin yadda jamiyyunsu za su fuskanci zaben 2015 da ke zama mai daukan hankalin al'ummar Najeriyar da ma kasashen waje don fatar an yi a wanye lafiya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita :Zainab Mohammed Abubakar