1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Fargabar tsaro yayin zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 29, 2018

Ana fargabar barkewar rikici a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, musamman a yankunan da aka dage zabe zuwa watan Maris. Rahotanni sun nunar da cewa jam'iyyun adawa sun fi tasiri a wadannan yankuna da aka dage zabukan.

https://p.dw.com/p/3Ale3
Kongo Beni | Protest & Demonstration gegen Ausschlus von Wahl
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Duk da cewa Shugaba Joseph Kabila ya ce ba zai sake tsayawa takara ba, sai dai ya kaawo dan takarar da zai maye gurbinsa, abin da ake wa kallon tamkar yana shirin ci gaba da yin mulki a bayan fage. 'Yan takara uku ne suka fi shahara cikin 'yan takara 21 da ke neman daarewa kan karagar shugabanci a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon da ke zaman kasa ta biyu mafi girma a Afirka. Daga cikinsu akwai na hannun daman Shugaba Joseph Kabila da ya kawo domin ya gaje shi Emmanuel Ramazani Shadary da ke da shekearu 58 a duniya. Goyon bayan da yake da shi na shugaba mai ci dai, ka iya sanya shi ya lashe zaben. Shadary dai na fuskantar tuhumar take hakkin dan Adam shi da wasu mutane 13 daga kungiyar Tarayyar Turai EU, abin da ya sanya ta kakaba musu takunkumi. Shi ma dan takarar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi mai shekaru 55 a duniya na fatan lashe zaben. Koda yake Tshisekedi da aka yi wa shaidar son zaman lafiya da fahimtar juna, ya yi kokari wajen bin sahun wasu 'yan takara daga bangaren adawa su shida da nufin marawa jagoran adawa Martin Fayulu baya, sai dai hakan bai samu ba, abin da ya sa Tshisekedi da Vital Kamerhe da shi ma ke zaman jagora a tafiyar adawar suka balle tare da hada karfi waje guda. Sai duk da haka Fayulu bai karaya ba, domin kuwa yana ganin shi ne zai lashe zaben, koda yake ya yi zargin cewa Kabila na son yin magudi.

Martin Fayulu
Hoto: Getty Images/AFP/T. Charlier

Koda a ranar Jumma'ar da ta gabata ma, sai da 'yan adawa suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da batun dage zaben a yankunan Beni da Butembo da kuma Yumbi, yankunan da hukumar zaben kasar CENi ta ce ba za a gudanar da zabuka a cikinsu ba, sai cikin watan Marsi na shekara mai kamawa ta 2019. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci duka bangarorin da su kai zuciya nesa, yayin da kungiyoyi kasa da kasa da ke rajin kare hakkin dan Adam suka zargi mahukuntan Kampala da amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zangar kamar yadda Abdoul Aziz Thioye jagoran hadakar kungiyar kare hakkin dan Adam da ke cikin tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Monusco a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ya nunar. A hannu guda kuma, kakakin rundunar ta Monusco Nabil Cherkaoui ya nunar da cewa za su ci gaba da gudanar da sintiri su kuma mayar da martani cikin sauri idan bukatar hakan ta taso, domin kare rayukan fararen hula, musamman a yankunan da 'yan bindiga suke. Za dai a rantsar da sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon a tsakiyar watan Janairun shekara ta 2019 mai kamawa.