1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Babban lauya na son kawo sauyin siyasa

Salissou Boukari
October 9, 2017

Shahararren lauya a kasar Kamaru Akere Muna, mai fafutikar yaki da cin hanci da ke yankin da ake magana da harshen Turancin Ingilishi ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2018.

https://p.dw.com/p/2lVrO
Wahl in Kamerun Paul Biya
Hoto: AP

Barista Akere Muna mai shekaru 65 da haihuwa, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar ne a karshen makon da ya gabata inda ya yi kira ga 'yan kasar ta Kamaru ya zuwa girka sabuwar jamhuriya bisa tafarki na kyakkyawan mulki da bin dokoki, tare kuma da shan alwashin kawo karshen cin hanci da bangaranci, da ma almundahana da dukiyar kasa. Kuma ya yi tsokaci kan ayyuka na farko da zai sa gaba:

" Batu na farko dai shi ne hada kawunan 'yan kasar Kamaru, sannan a duba batun mata da matasa, domin kasar Kamaru shekaru 57 bayan samun mulkin kai mace daya ce kawai ta kasance jakadiyar kasar a kasashen waje, wannan abin takaici ne. Matasa ba su da wuri, babu ayyuka, sannan ba a san yadda wasu ke samun nasu matsayi a kasar ba, kuma batun har ma a cikin rundunar sojojin kasar, ga kuma babban kalubale na kiwon lafiya da ilimi da shari'a."

Kamerun - Proteste
Zanga-zanga na neman zama jiki a KamaruHoto: Reuters/J. Kouam

A shekara ta 2000 Barista Akere Muna wanda ya ke da ne ga tsohon firaministan kasar ta Kamaru Salomon Tandeng Muna, wanda kuma ya shugabanci kungiyar lauyoyi ta kasar Kamaru, ya kafa reshen kungiyar Transparency International a 2000, sannan a shekara ta 2005 ya zamanto mataimakin shugaban kungiyar da ke fafutikar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya baki daya. Sannan daga shekara ta 2008 zuwa 2012 ya kasance shugaban majalisar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da raya al'adu ta Tarayyar Afirka. Sai dai duk da cewa shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya bai sanar da aniyarsa ta tsayawa takara ba, amma kuma ana ganin idan har ya tsaya zai yi wahala wannan sabon dan takara ya kai labari, sai dai a cewar Barista Muna yanzu lokaci ya sauya.