1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali na kara yin muni a Kamaru

Abdul-raheem Hassan AH
March 8, 2020

An kwashe daran jiya ana tafka kazamin fada tsakanin 'yan aware na Ambazonia da kuma sojojin gwamnati a Bamenda da ke a arewa maso yammacin Kamaru.

https://p.dw.com/p/3Z3WW
Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Tun can da farko 'yan Ambazonia sun gargadi jama'a da ka da su fito a bikin ranar duniya ta mata da ya gudana (08-03-20) kafin cikin dare a kwahe sa'oi ana yin dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin da na 'yan awaren. Wakilin DW Baba Abdullahi ya ce 'yan awaren sun tayer da bam kirar gargajiya a tsakiyar garin wanda yanzu haka aka samu asarar dukiyoyi da kadarori, sai dai ba a tantance ba asarar.