1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar warware rikicin kasar Kamaru

Isaac Mugabi RGB/LMJ
November 19, 2020

A kasar Kamaru, malamin addinin Kirista Kardinal Christian Tumi da 'yan bindiga suka sako kwanan nan, ya ce nauyin samar da zaman lafiya a duk fadin kasar ya rataya ne a wuyan Shugaba Paul Biya.

https://p.dw.com/p/3lZ4d
Kardinal Christian Tumi aus Kamerun
Kardinal Christian Tumi da ya samu 'yancinsa bayan 'yan awaren Kamaru sun sace shiHoto: DW/E. Asen

Kardinal Christian Tumi ya bayyana hakan ne, a tattaunawar da ya yi da tashar DW. Malamin da ke da shekaru 90 a duniya, ya kuma yi bayani kan halin da ya tsinci kansa a lokacin da aka yi garkuwa da shi a ranar biyar ga wannan watan na Nuwamba da muke ciki, kafin daga bisani 'yan tawayen da suka yi garkuwar da shi su sako shi. 

Karin Bayani: Jama’a na tserewa daga yankin Ambazonia a Kamaru

Kardinal Tumi ya ce ya yi ta binsu cikin daji kuma burinsu da ma su kama mutum domin neman kudin fansa, amma ya ce shi da sauran mutanen da ke tare da shi da suka kama ba su tambaye su kudi ba, sai dai sun nemi bayanai daga gareshi: ''Ba su ce nai musu laifin komai ba, sai dai sun ce suna son kawai na musu bayani a game da muradun gwamnatin kasar ta Kamaru, ba wai na gwamnatin jam'iyya mai ci ba domin ni ba dan siyasa ba ne. Saboda haka ba su samu wani bayani daga wajena ba.''

Kamerun Präsident Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kamaru dai na fama da rigingimu na 'yan aware da ke son ganin an raba kasar, shekaru hudu kenan ana fama da tashe-tashen hankula. To ko ina mafita daga wannan rikicin, Kardinal Tumi ya ce duk yana hannun shugaban kasar: ''Eh abu na farko da ya kamata a yi a kawo karshen fadan, a nemi maslaha domin yara su koma karatu. Duk wannan na hannun shugaban Jamhuriyyar Kamaru. Saboda haka a bar sojoji su koma bakin aiki kuma matasa da ke da makamai su ajiye.''

Karin Bayani: 'Yan gudun hijirar Kamaru da aka manta da su

Da aka tambayi malamin addinin Kiristan, wa yake ganin zai iya wannan jan aiki na lallamin wadanda ke gwagwarmayar da makamai? Kardinal Tumi ya ce: "Akwai kalilan da suka riga suka amince da sulhu suka kuma ajiye makamansu, amma abu na farkon dai, a bayar da umarni na sojoji su koma bakin aikinsu kuma shugaban Kamaru ne kadai zai iya shi kadai ya isa.''

Matsalar yankin masu magana da harshen Turancin Ingilishi a Kamaru, matsala ce da ta dade tun kafuwar kasar. Sai dai rikicin da ya dabaibaye yankunan Ambazoniya da ke magana daTurancin Ingilishin, ya balle ne a shekara ta 2016, inda ya haddasa asarar rayukan mutane kusan 3,000 yayin da wasu fiye da dubu 500 suka yi kaura daga gidajensu.