1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci a jihar Arewa mai Nisa

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 28, 2021

Ma'aikatar tsaron kasar Kamaru ta bayyana cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun halaka sojoji biyar da wani mutum guda tare da raunata wasu sojojin uku da kuma mutum guda.

https://p.dw.com/p/3yABm
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Mutane da dama hare-haren Boko Haram ya tarwatsa a Najeriya da makwabtantaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Rahotanni sun nunar da cewa, harin ya afku ne cikin daren Litinin din da ta gabata, a kan iyakar kasar Kamaru da Najeriya da ke zaman makyankyasar kungiyar ta Boko Haram din. Wata sanarawa da aka karanta a gidan radiyon kasar, ta bayyana cewa mayakan na Boko Haram dauke da manyan makamai a sansanin sojojin da ke jihar Arewa mai Nisa a kan iyakar kasashen biyu. Sanarwar ta nunar da cewa an halaka mayakan, sai dai babu wani karin bayani. Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa, sama da mutane dubu 36 ne hare-haren 'yan ta'addan na Boko Haram ya halaaka mafi aksarinsu 'yan Najeriya, tun bayan bullar kungiyar da ke addabar Najeriyar da makwabtanta a shekara ta 2009.