Kamaru ta haye mataki na gaba na AFCON
January 31, 2022Masar da Senegal sun bi sahun Kamaru da Burkina Faso wajen tsallakawa zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafan Afirka da ke gudana a Kamaru. A ranakun Laraba (02.02.2022) da Alhamis (03.02.2022) ne za a gudanar da wadannan wasanni.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain ta ce dan wasa Adama Traore zai sake komawa kungiyar bisa aro daga kungiyar Wolverhampton da ke Ingila har zuwa karshen kakar wasannin da ke wakana, kuma akwai yuwuwar a samu matsaya kan komawa kungiyar ta Barcelona baki daya daga bisani.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila ta ce dan wasanta Mason Greenwood ba zai buga wasa ba nan gaba sakamakon koken da 'yan sanda suka samu na zargin sa da cin zarafin wata. 'Yan sandan sun tabbatar da fara bincike kan lamarin na dan wasan Mason Greenwood dan shekaru 20 da haihuwa.
An kammala gasar tennis ta ostareliya
An kammala gasar wasan tennis na Ostareliya cikin wani yanayi na annashuwa da yammacin ranar Lahadi. Da ma dai jama'a sun zaci cewa wasan ba zai kayatar ba, bayan da mahukuntan kasar s ka tasa keyar tauraron wasan Novak Djokovic bisa zargin shi da karya dokokin da suka shafi annobar COVID-19. Amma gasar ta bana ta kafa tarihi iri-iri ta kuma kayatar da duniya.