1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Shell zai biya diya ga wasu jama'ar yankin kudancin Najeriya

January 30, 2013

Sakamakon hukumcin da wata kotu a ƙasar Hollande ta yanke wacce ta yi watsi da ƙara huɗu daga cikin biyar da manoma da masu kamun kifi a yankin Naija Delta suka shigare

https://p.dw.com/p/17UDZ
Durch Öl verschmutzter See im Ogoniland, Niger-Delta. Copyright: Mazen Saggar, UNEP
Hoto: Mazen Saggar/UNEP

Manoman dai da masuntan suna zargin kamfanin mai na Shell da laifin gurɓata muhali a yankin Naijai Delta na Tarrayar Najeriya.Kotun ta ce uwar kamfanin man na Shell baki ɗaya dake a ƙasar ta Hollande , bata da hurumin hanawa rassanta ɓatama wasu.

A cikin ƙara guda biyar da ƙungiyoyin masu fafutukar kare muhali suka shigare da sunan al'ummar yanki.Ƙara ɗaya kwai kotu ta amince da shi ,shi ne ,na malalar man da aka samu a garin Ikot Ada Udo da ke a yankin kudancin Tarrayar ta Najeriya a shekarun 2006 zuwa 207.a kan sa kotun ta yanke hukumcin cewar kanfanin Shell reshen Najeriya ;zai biya kuɗaɗen diya ga manoma da masu kamun kifin da tsiyayar man ya lalatawa gonaki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu