1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Sabon salo a rikicin masarautu

Nasir Salisu Zango LMJ
December 11, 2019

Yayin da ake ci gaba da cece-kuce dangane da hukuncin babbar kotun Kano wanda ya sake dakatar da kafa sababbin masarautu a jihar guda hudu, gwamnatin Kanon ta fitar da sanarwar cewar wannan hukunci bai shafe ta ba.

https://p.dw.com/p/3UbUk
Nigeria - Emir von Kano - Muhammadu Sanusi II
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi IIHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Wannan batu dai na ci gaba da jawo cacar baki wanda masana da sauran al'umma ke cewar ba zai haifawar jihar Kano natija mai kyau ba. A ranar Talatar da ta gabata ne babbar kotun jihar Kano karkashin justice AT Badamasi ta yanke kwarya-kwaryan hukunci, inda ta dakatar da samar da sababbin masarautun da kuma duk wani yunkuri na ci gaba da kafa majalisar sarakunan a Kano. Wannan lamari dai na kara nuna tsamin dangantaka da ke tsakanin fadar masarautar Kano karkashin Sarki Muhammadu Sanusi na II da kuma fadar gwamnatin jihar karkashin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje. Kuma wani tuntube dadin gushi da ya zama abin da ka iya zama sabo da yi wai gawa da gatsine, wayewar garin yau gwamnatin ta Kano ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Kwamared Muhammad Garba ta bayyana cewar wannan hukunci na kotu bai shafi sarakunan da gwamnatin ta kirkira ba haka kuma mun zanta da kwamishinan shari'a na jihar Barrister Ibrahim Mukhtar wanda ke cewar aikin gama ya gama dan haka wnanan oda ba ta shafi abin da gwamnati ta rigaya ta aiwatar ba.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

Sai dai lauyoyi masu zaman kansu da dama dai na sukar fahimtar gwamnatin jihar Kanon da kwamishinan shari'arta, inda Barrister Umar Danbaito da ke zaman lauya mai zaman kansa a Kano ke cewa hukuncin ya shafi masarautun kuma wajibi ne a bi shi. Tuni dai wannan sa-toka-sa-katsin da ya ki ci ya ki cinyewa a Kano, ya fara haifar da yanayi marar dadi a jihar wand ka iya zama barazana ga tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma. Tuni dai lamarin yasa magidanta irinsu Abubakr Ibrahim ke rokon bangarorin biyu su mayar da takubbansu cikin kube. A nata bagaren kungiyar ci-gaban jihar Kano karkashin dattijo Alhaji Bashir Usman Tofa suka fitar da sanarwar sukar matakin gwamnatin na kacaccala masarautar tare da abin da suka kira yin amfani da ramuwar gayyar siyasa wajen rushe tarihin da ya haura shekara 110. To amma duk da wnanan gwamnatin Kanon ta cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya fitar, ta ce batun sababbin masarautun ba gudu ba ja da baya, tare da kiran jama'a da a zauna lafiya.