1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Sulhun Daurawa da gwamnan Kano

Nasir Salisu Zango LMJ
March 5, 2024

Bayan cece-kuce kan wasu kalamai na gwamnan jihar Kano a Najeriya ma su kama da jirwaye mai kamar wanka da suka sanya shugaban Hukumar Hisba ta jihar sauka daga mukaminsa, a karshe dai sun sulhunta har ya koma aiki.

https://p.dw.com/p/4dCAC
Najeriya | Kano | Gwamna | Injiniya Abba Kabir Yusuf | Hisba
Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Injiniya Abba Kabir YusufHoto: Kyusufabba/Twitter

An kawo karshen tashin-tashinar da ta kunno kai tsakanin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif da kuma babban kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar Malam Aminu Ibrahim Daurawa. Wasu kalaman gwamnan da ke kama da jirwaye mai kamar wanka ne dai, suka sanya kwamandan Hisbar yin fushi da tare da ajiye mukaminsa. Wannan lamari dai ya janyo zazzafar muhawara a ciki da ma wajen jihar, inda wasu ke ganin babu kuskure a kalaman gwamnan wasu kuma ke cedwa ya yi wa kwamandan gyara a bainar jama'a.

Najeriya | Kano | Hisba
Daga cikin aiyukan da Hukumar Hisbar ke yi a Kano, har da kama motocin dakon giyaHoto: AFP/AMINU ABUBAKAR

Saidai bayan shiga tsakani da Zauren Hadin kan Malaman Jihar Kano ya yi, an sasanta an kuma yafi juna. Tuni ma dai Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ya tabbatarwa da DW cewar komai ya wuce kuma zai koma aiki ba gudu ba ja da baya, ya koma bakin aikin nasa. A ta bakin Dakta Ahmed Sa'idu Dukawa da ke zaman sakataren zauren da suka shiga tsakanin, kiraye-kirayen al'umma ne ya karfafa musu gwiwa. Shi ma da yake bayani kan batun, mukaddashin babban Hukumar ta Hisba Dakta Mujahid Aminudden Abubakar ya bayyana matukar jin dadinsa kan abin da ya ce an murkushe shaidan din da ya kunno kai a tsakani.