1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kara yawan sojojin Jamus da Faransa a Mali

February 21, 2014

Shugaban Faransa ya bayyana matakin da Jamus ta dauka na tura karin dakaru Mali da cewa kakkyawar alama ce da kuma ke kan turbar da ta dace.

https://p.dw.com/p/1BDJR
Von der Leyen besucht Soldaten in Mali
Hoto: Reuters

Bari mu fara da jaridar Der Tagesspiegel wadda a labarinta mai taken sojojin Jamus da na Faransa ga kasar Mali, cewa ta yi:

"Kasashen Jamus da Faransan sun amince da tura karin dakarun hadin guiwa zuwa kasar Mali mai fama da rkici da ke yammacin Afirka. A taron majalisar ministocin kasashen biyu karo na 16 da ya gudana ranar Laraba a birnin Paris, gwamnatocin kasashen biyu sun tabbatar da kara yawan sojojin a Afirka. Ko da yake tuni wani bangare na sojojin ke aikim karkashin inuwar tarayyar Turai EU a Mali, za a kara yawan sojojin Jamus a kasar ta Mali daga 180 zuwa 250, matakin da shugaban Faransa Francois Holland ya bayyana da cewa yana kan kyakkyawar turba. Tun a 1987 aka kafa wannan rundunar hadin guiwa mai sojoji 6000 na Jamus da kuma Faransa. Sun kuma gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashe kamar Bosniya da Afghanistan."

Hukuncin farko a Jamus ga kisan kare dangin Ruwanda

Ayyana laifi a shari'ar birnin Frankfurt game da kisan kiyashin Ruwanda inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

Onesphore Rwabukombe vor Gericht in Frankfurt 18.02.2014
Onesphore Rwabukombe a kotun birni FrankfurtHoto: imago/epd

"Tun da jimawa hukumomin shari'a a Ruwanda da na Majalisar Dinkin Duniya ke mayar da hankali kan kisan kare dangi da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a Kiziguro wani karamin yanki da ke Ruwanda a shekarar 1994. A ranar Talata hukumomin shari'a a Jamus sun yanke hukuncin farko kan wannan ta'asa. Wannan kuwa shi ne karon farko da wata kotu a Jamus ta yi zaman sauraron shari'a ga kisan kare dangin na Ruwanda. Babbar kotun jiha a birnin Frankfurt ta yanke hukuncin dauri shekaru 14 a gidan kaso ga Onesphore Rwabukombe dan shekaru 59, bisa rawar da ya taka a wannan kisa. A 1994 Rwabukombe wanda a 1985 ya sauke karatun fasahar gine-gine a nan Jamus, ya kasance magajin garin wani yanki na 'yan Hutu. Ko da yake bai fito fili ya ba da umarni da a kashe 'yan gudun hijirar Tutsi a lokacin ba, amma kasancewarsa a wurin a matsayin dan kallo, ya karfafa guiwar sojojin sa kai da suka aikata kisan kare dangin, inji kotun ta birnin Frankfurt."

Hatsari a ramin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi a kan mummunan hatsari da ya rutsa da masu hakar gwal ta haramtacciyar hanya a Afirka ta Kudu.

Minen-Unglück in Südafrika
Aikin ceto a hatsarin wurin hakar ma'adanaiHoto: picture-alliance/dpa

"Yayin da dubban masu aikin hakan ma'adanan ta barauniyar hanya, ke shiga wuraren hakan ma'adanai da aka daina amfan da su don hako abin da ya saura daga ciki, wasu ma'aikatan kamfanoni suna sumogar dutsi mai daraja ne don sayarwa a kasuwannin bayan fage. Da alamu wannan aiki mai hatsari yana da riba ga masun yinsa, domin a cewarsu suna samu makudan kudade fiye da karamin ma'aikaci a Afirka ta Kudu. Akasarinsu dai 'yan ci-rani ne daga kasashen makwabtan Afirka ta Kudu, wato irinsu Zimbabwe, Lesotho da kua Mozambik, wadanda ke shiga kasar saboda dalilai na tattalin arziki. Rashin kyakkyawan matakin kare lafiyar ma'aikata na faruwa hatta a wuraren hakan ma'adanai masu lasisin aiki."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe