1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karbar sabuwar gwamnati cikin bashi a Najeriya

Ubale MusaMay 6, 2015

A cewar sabbin gwamnonin da aka zaba da biyu gwamnatin da ta gaji kusan dalar Amirka miliyan dubu bakwai kuma ke shirin karewa da dinbin bashi ga kasar.

https://p.dw.com/p/1FLBE
Nigeria Goodluck Jonathan Abdulsalami Abubakar Muhammadu Buhari
Shugaba Jonathan mai shirin mika mulki da Janar Buhari mai shirin karbaHoto: DW/Ubale Musa

Kasa da tsawon 'yan makonni ga kaiwa ga fara sabuwar rawa a cikin tarrayar Najeriya, daga dukkan alamu har yanzu tana kasa tana dabo ga jam'iyyar APC da ke murnar samun mulki amma kuma ke neman kama hanyar fara aikin cika alkawari.

Kama daga shi kansa shugaban da ke shirin hawa gado, da ya zuwa gwamnonin jam'iyyar 22 dai hankula na tashe ga jam'iyyar mai alkawurin sauyi cikin kasa amma kuma babu kudi na tabbatar da kaiwa ga iyawa.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Buhari da 'yan jam'iyyarsa ta APCHoto: Chris Stein/AFP/Getty Images

Wani taron gwamnonin jam'iyyar da shugaban da ke jiran gado dai ya kare tare da korafi a bangaren gwamnonin da ke fadin suna shirin hawa gado ba tare ko sisin fara aiyyukan al'umma ba.

Ya zuwa yanzu dai sai da ta kai kasar ga cin bashin kusan Naira Miliyan dubu dari hudu kafin iya kaiwa ga yunkurin biyan ma'aikata a wani abun da ke zaman alamar rushewar lamura yanzu.

Abun kuma da ya tada hankalin gwamnonin da suka ce da biyu ga gwamnatin da ta gaji kusan dalar Amirka miliyan dubu bakwai kuma ke shirin karewa da dinbin bashi ga kasar.

Abun kuma da ake dangantawa da katobarar wasoson da ya biyo bayan yunkurin shugaban kasar na sake darewa kan mulki.

Yunkurin kuma da a majiyoyi suka ce ya kai kasar ga asarar kusan kaso 50 cikin dari na kasafin kudin kasar na shekarar bana.

Sabuwar matsalar rashin kudin dai na zaman kalubale mafi girma ga gwamnatin da ke da dimbin buri a zuciya.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Anhänger Jubel
'Yan Najeriya na buduri bayan nasarar BuhariHoto: picture-alliance/AP/J. Delay

Abun kuma da a tunanin Dakta Nazifi Darma da ke zaman masanin tattalin arziki ya sanya zama mafita ga sabuwar gwamnatin na rungumar sabbabi na dabaru da nufin sauya kasar a cikin lokacin da ke akwai:

To sai dai kuma ko bayan batun na jari na waje dai sabuwar gwamnatin na da burin sake kaddamar da bincike kan masana'antar mai ta kasar da nufin sake kwato kudaden da ake zargi da kwashewa tare da kaisu ga aljihuna na kalilan.

Sama da dalar Amirka miliyan dubu 20 ne dai ake takaddamar kwashewa a masana'antar da ke zaman jini da tsoka ta kasar, abun kuma da a cewar Dakta Kole Shetima da ke zaman shugaban cibiyar tabbatar da demokaradiya da cigaba zai zamo dan ba mai kyau ga sabuwar gwamnatin kasar a halin rashin kudin.