1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantakar Afirka da Turai

Mohammad AwalApril 2, 2014

Batun rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya mamaye taron karfafa dangantakar Tarayyar Turai da kasashen Afirka na yini buyu da ake gudanarwa a birinin Brussels.

https://p.dw.com/p/1BaQA
Hoto: Reuters

Kasashen kungiyar ta EU dai sun alkawarta kara karfin tallafin da suke baiwa nahiyar Afirka a fannin tsaro da kuma bunkasa huldar kasuwanci a yayin taron da suke gudanarwar a birinin na Brussels na kasar Belgium. Da ma dai muhimman abubuwan da suke sahun gaba a dangantakar da ke tsakanin kasashen nahiyar Afirka da kuma kungiyar Tarayyar Turan sun hadar da batun samar da zaman lafiya da kasuwanci da zuba jari da ilimi da fannin lafiya da kuma bada tallafi ga kungiyoyin farar hula.

Daga shekara ta 2004 kawo yanzu kungiyar ta EU ta kashe sama da biliyan daya na kudin Euro wajen tallafawa shirin samar da zaman lafiya a kasashen Afirka da suke fama da rikici da suka hadar da Jamhuriyar Dimokaradiyar Kongo da Sudan da Sudan ta Kudu da Somaliya da Mali da kuma Jamhuriyar Afirka ta TSakiya. A jawabin da ya yi a gefen taron, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai da kuma kasashen Afirka da su kara kaimi wajen ganin sun shawo kan rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da yake neman komawa yakin kisan kiyashi.

Zuba jari da kuma inganta zaman lafiya

Taken taron na bana dai shi ne "zuba jari a fannin ci-gaban al'umma da kuma zaman lafiya". Da suke jawabi a wajen taron shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun bayyana shirin da suke da shi na inganta dangantaka da kasashen Afirka a fannin tsaro da ci-gaban al'umma da kuma dumamar yanayi. A jawabinsa Shugaba Francois Holland na Faransa ya bayyana cewa Faransan da Jamus za su yi aiki tare a kan wadannan fannonin uku. Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi kamata ya yi bayan batun magnace tashe-tashen hankula, kungiyar EU din ta inganta dangantakar kasuwanci da kasashen Afirkan tana mai cewa....

Angela Merkel und Francois Hollande beim EU Afrika Gipfel in Brüssel
Shugabar gwamnatin Jamsu Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Francois Hollande a wajen taronHoto: Reuters

"Nayi farinciki da muka kasance tare a nan kuma za muyi aiki tare da kawayenmu kasashen nahiyar Afirka. Za mu yi aiki domin taimaka musu wajen ci gaba da kuma shawo kan mastalolin yankin. A yanzu haka muna aiki tare da su domin taimaka musu wajen shawo kan matsalolin da suka addabesu".

Shin ko ya ya shugabannin Afirkan suke ganin wannan kokari na inganta dangantakar da ke tsakaninsu da kungiyar ta EU? Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou ya yi karin haske.

"Ai nasan kun san taken wannan taro dan a yi nazari ne bisa tsaro da kwanciyar hankali da ci-gaba, sannan da batun bunkasar al'umma. Kuma abun da nake jira da wannan taro shine Tarayyar Turai ta ci gaba da kasance wa kusa da kasashen Afirka kunsan Tarayyar Turai ita ce abokiyar huldar mu ta farko. Dan haka yana da mahimmancin gaske huldar dake tsakanin mu taci gaba. Ku tuna fa a babban taron da aka yi na birnin Lisbone mun yi tsari da baki guda wanda a halin yanzu aka fara ganin sakamako dan haka muna son abun ya ci gaba musamman ma batun bunkasar kasashe ya kasance sahun gaba."

EU Afrika Gipfel in Brüssel 02.04.2014
Zauren taron EU da AfirkaHoto: Reuters

Alkawarin inganta dangantaka da Afirka

A nasa jawabin sakataren harkokin kasashen ketare na Birtaniya William Hague ya bayyana farin cikinsa da wannan taro inda ya ce Birtaniya za ta kara karfafa huldar kasuwancin dake tsakaninta da nahiyar ta Afirka.

"Wannan wani abun farin ciki ne da muka kasance tare da kawayenmu kasashen Afirka domin inganta dangantakar dake tsakanin kungiyar EU da kuma Afirkan. Birtaniya za ta kara inganta dangantakar kasuwanci da Afirka muna bude sababbin ofisoshin jakandanci a can muna kuma kara karfafa huldar diplomasiyya da su domin kuwa daya daga cikin yankin da tattalin arzikinsa ke bunkasa cikin hanzari yana nahiyar Afirka ne".

Kimanin shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai wato EU da kuma na nahiyar Afirka 70 ne ke halartar wannan taron da ake sa ran za su amince da yin kasuwanci ba tare da haraji ba a tsakanin bangarorin biyu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal