1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa taimako ga 'yan tawayen Siriya

February 28, 2013

Babban taron kasashen duniya a birnin Rom zai tattauna kan ba wa 'yan adawar Siriya taimako don cimma burin kawo sauyin shugabanci a kasar.

https://p.dw.com/p/17nSG
Demonstrators chant slogans and wave Syrian opposition flags during a protest against Syria's President Bashar al-Assad in Bustan al-Qasr district in Aleppo February 22, 2013. REUTERS/Muzaffar Salman (SYRIA - Tags: CONFLICT POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

A wannan Alhamis kasashen nan dake kiran kansu aminan Siriya za su gudanar da wani babban taro a birnin Rom na kasar Italiya domin nemo mafita ga rikicin kasar ta Siriya. Bayan adawa da ta nuna da farko, babbar kungiyar 'yan adawar Siriya za ta halarci taron, inda za a kuma tattauna a kan irin taimakon da za a ba wa masu ta da kayar baya a kasar. Sabon sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry wanda shi ma zai halarci taron ya ce, gwamnati a Washington na neman hanyar da za a gaggauta samun sauyin siyasa.

"Dole Assad ya san cewa bai da mafita daga wannan rikicin. 'Yan adawa kuma na bukatar karin taimako don su cimma wannan buri. Shi ya sa muna aiki tare domin samun matsaya guda a kan wannan batu."

Jaridar Washington Post da kuma tashar telebijin ta CNN sun rawaito cewa gwamnatin Amirka na duba yiwuwar ba wa 'yan tawayen Siriya makamai ciki har da motoci masu sulke da kuma horo irin na soji. Kawayen Siriyar dai sun hada da kasashen yamma da na Larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle zai wakilci kasarsa a gun taron.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar