1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cudanya tsakanin likitocin Masar da Najeriya

Abdourahamane Hassane
May 24, 2019

Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke a Labai Najeriya ta kulla yarjejeniyar da jami'ar Mansura ta Masar domin yin cudanya a fannin aikin likita.

https://p.dw.com/p/3J2us
Ägypten Kairo Proteste Verletzte
Hoto: picture-alliance/dpa

Musanya ta dalibai daga jami'o'i a fannin kiwon lafiya daga wata jami'a zuwa wata jami'ar don karin ilimi ya kan taimaka sosai wajen samun kwarewa da kuma kara fahimta a daidai lokacin da sabbin na'urori na kula da sha'anin kiwon lafiya ke kara bazuwa a duniya. Wannan yarjejeniya da jami'o'in biyu suka kulla za ta bai wa daliban kasashen damar daukar ilimi a Najeriya da Masar, abin da zai taimaka wajen kawo ci-gaba ga sha'anin kiwon lafiya a kasashen biyu.