1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hare-haren ta'addanci a Mali

Gazali Abdu TasawaApril 16, 2015

Ayyukan 'yan tarzoma da ke karuwa a Mali na barazanar yin mummunan tasiri a kan rayuwar al'ummar kasar da ma shirin yin sulhu.

https://p.dw.com/p/1F9gt
Mali Konflikt französischer Soldat Gao Frankreich
Hoto: Reuters

Yanzu haka wasu 'yan kasar Mali sun soma tofa albarkacin bakinsu a kan harin da wasu 'yan ta'adda suka kai a kan sojojin rundunar tsaron lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato Munisma da ke a garin Asango.

Harin wanda na kunar bakin wake ne da aka kai da mota a cibiyar rundunar tsaron zaman lafiyar ta Munisma a Mali shi ne hari na farko da aka kai a cikin 'yan watannin baya-bayan nan a garin na Asango. Sojojin rundunar ta Munisma uku ne dai suka rigamu gidan gaskiya a yayin da wasu mutane 16 da suka hada da sojojin Nijar tara suka jikkata. Sai dai a cewar Malam Suleimane Umaru wani dan kasar ta Mali mazaunin garin na Asango, wannan hari bai zo masu da mamaki ba.

"Wannan hari a cikin garin Asango bai ba mu mamaki ba saboda ko da yaushe gari ne da ke da 'yan ta'adda. Misali ka dauka daga Menaka zuwa Gawo ko kuma daga Asango zuwa Nijar wajeje ne da ko da yaushe a kan iya samun faruwar hare-hare a cikinsu sabili da yaduwar kungiyoyin 'yan ta'adda a cikinsu."

Mali UN in Kidal
'Yan ta'adda na yawaita Kai hari a kan motocin da ke bi cikin HamadaHoto: Fabien Offner/AFP/Getty Images

Babban kwamandan rundunar zaman lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali Hongi Hamdi ya yi tir da Allah wadai da wannan hari, wanda ya ce ba zai sa su kariya ba a cikin aikinsu na tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Asango na da muhimmanci ga 'yan kasuwa

Sai dai Malam Suleimane Umaru mazauni garin na Asango ya bayyana fargabarsa a game da tasirin da wanann hari zai yi ga harkokin kasuwancin wannan gari da sauran kasashe makobta irinsu Nijar.

"'Yan kasuwa da ke tasowa daga Nijar zuwa Gao sai sun bi ta Asango ko kuma daga Gao zuwa garin Menaka shi ma sai ka biyo ta Asango. Kuma wadannan hanyoyi masu hadari ne 'yan kasuwa suke bi su kawo kaya. Ke nan ka ga irin wadannan hare-hare na haifar da tsoro a zukatan 'yan kasuwa. Ka ga in irin haka na faruwa ke nan babu zancan kasuwanci."

Fatan yin sasantawa don samun zaman lafiya

Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da bangarorin da ke hamayya da juna a Mali ke zaman sasantawa a garin Algiers da zumar gano bakin zaren warware matsalar. Batun da Malam Suleimane Umaru ya ce suna da kwarin gwiwar za a ciwo kansa domin a halin yanzu a kasar ta Mali an shiga cikin irin hali na biri ya gaji mai gona ya gaji.

Algerien Mali Waffenruhe in Algier vereinbart Bilal Ag Acherif Tuarega
Wakilan Abzinawa a tattaunawar neman sulhuHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

"Ina ganin hare-haren da ake fuskanta ba zai hana sasantawa ba. Sabili da a yau akwai mutane da yawa da sun gaji suna son a sansanta. Alal misali akwai ma'aikatan gwamnati da ba sa samun albashi kuma ba aiki. Ka ga suna son a sasanta don su samu kanunsu. Don haka a yanzu al'umma duk wanda ka tarba za ka ji fatansa shi ne a samu a sasanta don komi ya koma daidai."

A shekara ta 2012 ne dai kungiyoyin da ake kira na 'yan ta'adda rassan kungiyar Al-Qa'ida suka mamaye kasar ta Mali kafin daga baya sojojin taron dangi a karkashin jagorancin kasar Faransa su kore su daga wasu yankunan. Sai dai yanzu haka sassa da dama na yankin arewacin Mali ba sa a karkashin ikon gwamnatin kasar, inda a nan ne mayakan tsagerun suka samu mafaka suna kuma kaddamar da hare-hare lokaci zuwa lokaci a kan sojojin Majalisar Dinkin Duniya.