1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kin jinin baki a Jamus na karuwa

Sabrina Pabst/Usman Shehu Usman/YBAugust 27, 2015

Cikin 'yan kwanakin nan ana kara samun batagari da ke kai farmaki kan baki saboda kyama, abin yafi faruwane a Gabashin Jamus, inda aka samu kashi 61 cikin dari na daukacin hari kan bakin.

https://p.dw.com/p/1GMtw
Deutschland Gauck besucht Flüchtlingsunterkunft in Berlin Wilmersdorf
Shugaba Gauck na Jamus cikin fara'a a ziyarar 'yan gudun hijiraHoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Ba a raba daya biyu dai kungiyar masu kyamar baki da aka sani da PEGIDA, ta kunna wutar kyamar baki a jihar Sachsen, ko da yake baza a manta da cewa a jihohin Yammacin kasar dama 'yankin Bavariya, dama jihar Bade- Wütenberg suma an samu rahotannin kona wuraren da 'yan gudun hijira suka fake, amma dai lamarin kungiyoyin bata gari da ke kyamar baki yafi karfi ne a jihar ta Sachsen da ke Gabashin Jamus. Hans-Joachim Maaz wani masanin halayen bil'adama ne.

Deutschland Flüchtlinge in Heidenau
'Yan gudun hijira a HeidenauHoto: Reuters/M. Rietschel

"Idan muna batun kan kyamar baki, zan iya cewa matsalace ta daukacin kasar Jamus dama Turai baki daya, a yanzu anan samun masu tsananin kin baki, musamman 'yan gudun hijira, kuma lamari na fitowa ne daga bangaren kungiyoyi dama jam'iyyu dama masu wa'azin addini. Ta ko wane bangare ana samun dai-daikun mutane da kuma kungiyoyi da ke matukar kyamar baki, batun ya zama kamar cuta."

To amma ayar tambaya ita ce menene dalilin da yasa a yankiin jihar Sachsen da ke Gabashin Jamus aka fi samu matsalar da ta shafi kyamar baki, masanin ya yi karin haske.

"A Gabashin Jamus batun ya samo asali da matsalolin sake hadewar Jamus ta Yamma da ta Gabas. A shekara ta 1989, hadewar kasashen biyu a matsayin kasa daya bai kai ga samun sake sajewar al'ummomin a matsayi guda ba. Wannan matsalar ta biyo iyalai da dangi ne, kuma hakan ya sa matasa manyan gobe sun gaji wannan muguwar dabi'a. Kiyayyar tasu wani abu ne kamar na huce haushi musamman kan 'yan gudun hijira domin su ne suka samu kansu a wata matsala ta rayuwa".