1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar muhawara kan baki da addini a Turai

Mohammed Nasiru AwalJanuary 13, 2015

A yan wataninnan ana yawaitar samun gangami a biranen Turai daban-daban bisa goyon baya ko adawa da lamarin da ya shafi baki ko addini.

https://p.dw.com/p/1EJbg
Dresden Pegida Demonstration 12.01.2015
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Burgi

Tun a cikin watan Oktoban bara a kowace ranar Litinin a birnin Dresden na gabashin Jamus masu kyamar baki da ke kiran kansu Pegida ke gudanar da zanga-zangar adawa da yaduwar Musulunci a nahiyar Turai. Sai dai a macin da suka yi jiya Litinin da ke zama mafi girma ya zuwa yanzu, ya gamu da gangamin adawa da Pegida mafi girma a wasu biranen Jamus, ciki har da Leipzig da ke gabashin Jamus da kuma wasu birane irinsu Munich da Düsseldorf.

Mutane fiye da dubu 25 magoya bayan Pegida suka yi maci a cikin birnin na Dresden da yammacin ranar Litinin, inda suka gamu da gungu-gungun masu adawa.

Jawabin da ya yi gabanin macin, mai shirya macin kuma mai magana da yawun Pediga, Lutz Bachmann ya ce abubuwa guda shida kungiyar take son cimma da suka hada da: Samar da wata dokar zaman baki da 'yanci da kuma alhakin sajewa da 'yan kasa da korar masu kaifin kishin Islama da sauran addinai, da samar da cikakken tsaron kasa.

München Anti-Pegida Demonstration 12.01.2015
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Hase

Kungiyar ta yi amfani da lamarin da ya faru makon jiya a birnin Paris inda wasu 'yan bindiga suka kai hari kan kamfanin buga wata mujallar barkwanci, don karfafa matsayinta a macin na ranar Litinin, da ke zama na farko tun bayan harin na Paris. Sai dai kungiyoyi da 'yan siyasa sun yi tir da hakan suna cewa Pegida na son ta yi amfani da halin da ake ciki don cimma manufofinta. Heiko Maas shi ne ministan shari'a na Jamus.

Ya ce: "A makon da ya gabata Pegida ta zargi 'yan jarida da cewa makaryata ne, amma yanzu sun bazu kan titi wai su suna nuna alhini ga 'yan jarida. Wannan manufunci ne babba."

Shi ma ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya zargi Pegida da kokarin amfani da hare-hare a kan kamfanin mujallar Charlie Hebdo don cima manufofinta na siyasa.

Gabanin gangamin na ranar Litinin Pegida ta wallafa a shafinta na Facebook cewa Mr Maas ko masu adawa da kishin kasa ba za su iya dakatar da su ba.

Yanzu haka dai ana samun karuwar yawan Jamusawa da ke nuna adawa da Pegida. Ko a ranar Asabar da ta gabata mutane kimanin dubu 35 masu adawa da Pegida sun yi gangami a gaban majami'ar birnin na Dresden. Sannan a birnin Leipzig da ke gabashin addu'o'in neman zaman lafiya aka gudanar a cocin Nikolai gabanin fara wata zanga-zanga mafi girma a Jamus don nuna adawa da Pegida, inda mutane fiye da dubu 30 da suka hada da kawancen coci da kungiyoyin ma'aikata da sauran jama'a kamar wannan matar suka yi maci cikin birnin.

München Anti-Pegida Demonstration 12.01.2015
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Hase

Ta ce: "Mutane da yawan gaske suka hallara inda suka fito fili suka kudurinsu ta hanyar yin zanga-zangar lumana don adawa da Pegida da manufar kyamar baki."

A birnin Munich da ke kudancin kasar mutane kimanin dubu 20 ne suka bazu kan titi suna tir da Pegida da masu kyamar Musulunci. Sun rike tutocin adawa da kyamar baki da Yahudawa. A Düsseldorf ma haka abun ya kasance, inda ake kokarin hana wata mummunar gaba tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba a Jamus bayan hare-haren birnin Paris.

Da yammacin wannan Talata shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel da shugaban kasar Joachim Gauck za su halarci wani gangami a birnin Berlin da al'ummar Musulmin kasar suka shirya don nuna muhimmancin zaman tare da adawa da harin da aka kai a birnin Paris sannan su mika sako ga dubban masu adawa da yawaitar Musulmi a kasar.