1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar 'yan gudun hijira a Jamus

Zainab Mohammed AbubakarDecember 10, 2015

Wani na kusa da shugabar gwamnatin Jamus, ya yi kira da a tura 'yan sandan kula da kan iyaka zuwa iyakokin Turai, domin taimaka wajen rage yawan 'yan gudun hijira

https://p.dw.com/p/1HLat
Griechenland Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

Volker Kauder da ke shugabantar 'yan majalisar jam'iyyar CDU na Merkel ya yi wannan furucin ne, gabannin taron jam'iyyar ta kasa a mako mai zuwa, taron da ake saran mahawara akan 'yan gudun hijirar ce za ta mamaye shi.

Bugu da kari dan majalisar Jamus din ya kuma nemi Kungiyar Tarayyar Turai da ta nada mukamin kwamissionan kula da kan iyakokinsu na ketare. Babban kuduri da za'a gabatar a taron yinu biyu na jam'iyyar CDU a birnin Kalsruhe da ke yammacin Jamus dai shi ne, bukatar kasashen na Turai su hada kai domin warware matsalar 'yan gudun hijira.

Kudurin na kuma nuni da cewar, ba za'a iya warware matsalar masu neman mafaka na siyasa a mataki na kasa ba. Sai dai takardar bata mabaci adadin 'yan gudun hijirar da kasar za ta karba ba, wadda ake zato za su shige miliyan guda.