1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Faransa ta ce bata bukatar zama a Mali

Usman ShehuFebruary 6, 2013

Kasar Faransa ta bada tabbacin cewa za ta fice daga kasar Mali da zaran al'amura sun lafa

https://p.dw.com/p/17Zqb
France's President Francois Hollande (C), flanked by French Foreign Affairs Minister Laurent Fabius (Back-3rdL) and French Defence Minister Jean-Yves Le Drian (Back-2ndL) shakes hands with Prefects of Mopti upon his arrival at Sevare, near Mopti, on February 2, 2013. President Francois Hollande visits Mali as French-led troops work to secure the last Islamist stronghold in the north after a lightning offensive against the extremists. Hollande will head to Timbucktu and Bamako. AFP PHOTO / PASCAL GUYOT (Photo credit should read PASCAL GUYOT/AFP/Getty Images)
Francois Hollande, shugaban kasar Faransa a ziyarar da ya kai MaliHoto: Pascal Guyot/AFP/Getty Images

Kasar Faransa a rubece ta bukaci MDD a tura rundunar kiyaye zaman Lafiya izuwa kasar Mali, da zaran sojan Faransa sun fice daga kasar ta Mali, idan al'amura suka lafa. Jakadan kasar Faransa a MDD Gerard Araud ya fadawa zauren kwamitin sulhu na MDD mai wakilai 15 da su bada izinin tura dakaru karkashin majalisar, kuma yace ya samu tabbaci daga kasashe masu wakilci, za a amince da bukatar kasar ta Faransa. Jakadan ya kara da cewa dakarun kasarsu ba za su ci gaba da kasan cewa a kasar Mali ba, don haka sai dai kawai ana bukatar dai-daituwar al'amura kafin isar dakarun na MDD. A dole ne bisa doka Kasar Mali da kanta ta bukaci a tura dakarun na MDD izuwa kasar ta, duk da cewa akwai adawa da kasan cewa dakarun ketari a tsakanin yan kasar ta Mali.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu