1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Sao Tome na fama da rikicin zabe

Abdul-raheem HassanAugust 2, 2016

A daisai lokacin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Sao Tome, shugaba mai ci ya ce ba zai shiga a dama da shi ba.

https://p.dw.com/p/1JaWD
Manuel Pinto da Costa
Hoto: Ramusel Graca

Shugaban Sao Tome da Principe mai ci a yanzu Manuel Pinto da Costa ya ki shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa sakamakon abin da ya danganta da magudin da aka tafka a zagayen farko. Cikin wata wasika da ya aika wa kotun tsarin mulki, mista Pinto da Costa da ya zo na biyu ya na neman a soke sakamakon zaben tare da shirya wani sabon zabe. Sai dai kotun tsarin mulkin kasar da ta rigaya ta bayyana sakamakon dindindin na zagayen farko ta ce ba zata lashe amanta ba.

Tun da farko dai hukumar zaben kasar ta Sao Tome ta fara bayyana abokin adawa shugaban kasa wato Evaristo Carvahlo a matsayin wannan ya ke kan gaba da yawan kuri'u, kafin daga bisani ta kwaskware alkalumanta. A ranar 5 ga watan Agusta ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben.

A wannan kasa ta tsakiyar Afirka wacce dimukradiyya ta samu giidn zama tun shekaru 25 da suka gabata, shugaban kasa mukami ne na jeke na yi ka, saboda Firaminista ne ke da wuka da nama na tafiyar da harkokin mulki.