1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Thailand ta alkawarta tura sojojinta Darfur

October 10, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8m

Kasar Thailand ta alkawarta tura dakarunta 800 zuwa lardin Darfur na kasar Sudan nan gaba cikin wannan shekarar.

Maaikatar harkokin wajen kasar ta sanarda da cewa majalisar zartaswa ta amince da tura wadannan dakaru da zasu yi aiki karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya na hadin gwaiwar MDD da AU su 26,000 da ake shirin turawa Darfur.Sanarwar tace zasu kasance a darfur na tsawon watanni 12.

Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen Thailand Tharit Charungvat yace wannan yana bangare ne na nauyi daya rataya a wuyan kasar na taimakawa a harkokin duniya.

Thailand tace zata kashe fiye da dala miliyan 10 wajen daukar nauyin dakarun nata a farkon watanni shida na aiyukansu a darfur sai dai kuma MDD zata biya ta daga bisani.