1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Yamen na shan luguden wuta

Yusuf BalaMay 10, 2015

Jiragen yaki Saudiyya a sun yi ruwan bama-bamai a gidan tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh abinda ke nuna fada yakin da kasar ta kaddamar don kwace iko.

https://p.dw.com/p/1FMdU
Jemen Sanaa Zerstörung Ruine Menschen
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Hakan dai ya faru ne bayan wani lugudan wuta da Saudiyyar ta yi a yankin da mayakan Houthi suka ja daga, kamar yadda wani da ya ga yadda lamarin ya faru ya shaidar.

Jiragen yaki biyu ne dai suka kai farmaki a wannan gida na tsohon shugaba Saleh, mai karfin fada a ji a siyasa kasar. Wannan gida kuma na shugaba Saleh na a tsakiyar birnin Sanaa ne fadar gwamnatin kasar ta Yemen, a lokacin kai wannan hari shugaban baya cikin daga birnin.

Shugaba Ali Abdallah Saleh dai, ya sauka daga kujerar mulkin kasar ne, a watan Fabrairu na shekarar 2012, bayan wata zanga-zangar adawa da ba ga irinta ba a tsawon mulkinsa na shekaru 30.

Kazalika ana zargin tsohon shugaban da daukar bangare, a rikicin da kasar ta Yemen ta fada. In da ya ke mara baya ga bangaren mayakan Houthi da ke zama 'yan Shi'a wadanda ba sa ga maciji da shugaba Abedrabbo Mansour Hadi, wanda don shi ne Saudiyyar ke kai hare-haren bama-bamai na cewa dole sai ta mai da shi kan mulki.