1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka na neman magance matsalar tsaro

July 18, 2019

Gwamnonin jihohin da ke kewayen tafkin Chadi sun duba hanyoyin shawo kan matsalar tsaro da yankin ke fama da shi, yayin da manyan jami’an hukumomin leken asiri na Afirka suka nemi rage fitar da kudin haramun daga nahiyar

https://p.dw.com/p/3MH6o
Polizei in Nigeria
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Gwamnonin jihohin kasashe hudu da ke kewayen tafkin Chadi ciki har da Nijar da Najeriya da kamaru da Chadi sun tuntubi juna a birnin Yamai don tuna yadda za su kyautata harkokin kasuwanci da kamun kifi da rayuwar al'ummomi da ke rayuwa a wannan yanki. Wannan mataki na da nasaba da rikicin Boko Haram da ya salwantar da rayuka da barnatar da dukiya tare da sa dubban mutane kaurace wa matsugunansu da wuraren neman kudinsu. Hasali ma gwamnonin sun nemi agajin kungiyoyin da ke da hannu da shuni na duniya don su horas da 'yan gudun hijira sana'o'in hannu tare da ba su jari. Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka na daga cikin wadanda suka tura da wakilai a wannan taro.

Su kuwa shugabannin hukumomin leken asiri na kasashen Afirka sun gano a taron da suka gudanar a Abuja na Najeriya cewa akalla  Dalar Amirka miliyan Dubu 560 ne ake fitarwa daga nahiyar ta Afirka a duk shekara. Kuma sannu a hankali kungiyoyinta’adda na kara samun hanyoyin samar da kudaden na haramun. Kungiyoyi na ta’adda kamar  Boko ta Haram da al-Shabaab na amfani da kafofin sadarwa na zamani domin samun sabobbin magoya baya da kuma yada manufofinsu tsakanin al’umma na gari. Sun kuma kara fadada hanyoyin samunkudade ta hanyar karbar haraji a tituna , da kuma sai da ma’adinai irin su Zinare dama samun damar ikon tafi da harkokin teku da hanyoyin cinikin da ke a cikinsu.

Nigeria Abuja Geldscheine in verschiedenen Währungen
Kungiyoyin ta'adda na fitar daga kudi daga Afirka don sayan makamai a cewar kwararruHoto: DW/Katrin Gänsler

Jami'an leken asiri na kasashen Afirka suka ce dole ne a dubi hanyoyin dakile wadannan hanyoyin da ke samar da kudi ga kungiyoyin ta’adda. Daga shekarar 1980 zuwa shekara ta 2009, a fadar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, nahiyar Afirka ta yi asarar tsakanin tirilliyan daya da miliyan dubu dari biyu zuwa tiriliyan daya da miliyan dubu dari Hudu na dalar Amirka, abin da ke zaman kusan rabin daukacin arzikin kasashen na Afirka. A cewar mai masaukin bakin kuma shugaban tarrayar Najeriya  Muhammadu Buhari ya zama wajibi a samun sabobbin dabarun tunkarar matsalar da ke neman wucewa da sanin kundila .