1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai na sabbin shirye-shirye kan tsaro

January 21, 2015

Faransa da wasu jami'ai daga kasashen Turai zasu bayyana shirinsu kan matakan dakile ayyukan 'yan ta'adda a yau Laraba bayan sabbin barazana da ake samu biyo bayan hare-haren 'yan bindiga a birnin Paris.

https://p.dw.com/p/1ENag
Anti-Terror Kampf Bewaffnete Britische Polizisten
Hoto: AP

A babban birnin kasar ta Faransa an tsaurara matakan tsaro tun bayan harin masu Jihadi da yayi sanadin hallaka mutane 17 makwanni biyu da suka gabata, Firaminista Manuel Valls zai bayyana alkawuran matakan tsaro dan zama cikin kyakkyawan shirin ko ta kwana.

Wannan hari da ke zama mafi muni a kasar ta Faransa cikin shekaru gwammai ya sanya kasashe daga yankin na Turai kara tsaurara matakan tsaro.

Hukumar kungiyar Tarrayyar Turai za ta yi wani zama na musamman a birnin Brussel dan tattaunawa da mambobin kungiyar daga kasashe 28 inda zasu zayyana sabbin tsare-tsare kan yaki da masu tada kayar baya, ciki kuwa har da batun samar da sauyi ga tsarin takardar shiga kasashen na Turai mara shinge, da samar da bayanai na sirri tsakanin kasashen.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu