1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashe-kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

May 16, 2014

Wasu tagwayen hare-hare da 'yan bindiga suka kai a arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun salwantar da rayukansu mutane da dama tare da jikata wasu.

https://p.dw.com/p/1C1XK
Hoto: Reuters

Mutane uku suka rasa rayukansu yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wasu hare-harre da 'yan bindigan sa kai suka kai a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Waɗanda suka shaidar da lamarin sun bayyana cewar waɗanda suka aikatasu sun kwashi ganima, yayin da su kuma al'ummar garuruwan da ke kusa da garin Batangafo suka kaurace wa matsugunansu domin tsira da rayukansu.

Wani ɗan garin Batangafo inda waɗanda hare-haren ya shafa suka samu mafaka ya nuna takaicinsa dangane da aikata ta'asar da ake yi a gaban sojojin ƙasashen Afirka ta MISCA ba tare da sun ɗauki mataki a kai ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane