1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashe-kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 17, 2015

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane da dama a yankin Arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka T tsakiya ba tare da wani tartibin dalili ba.

https://p.dw.com/p/1Es6q
Hoto: AFP/Getty Images

Akalla mutane goma sun rigamu gidan gaskiya a yankin Arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yayin da wasu da dama kuma suka jikata, a wani harin da jami'an tsaro suka zargi 'yan bindigan kasar Chadi da kaiwa.

jandarmomin kasar suka ce tun kwanaki ukun da suke gabata ne wadannan 'yan bindiga suka kutsa garin Ngaoundaye inda suka yi ta aikata ta'asa a kan fararen hula. Ba a dai bayyana dalilin kai wannan hari ba. Amma kuma garuruwa da dama na arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun fuskance hare-hare daga 'yan bindiga a kwnakin baya-bayannan.

Sojojin kasashen Afirka da ke wanzar da zaman lafiya a wannan kasa sun fara sintiti a wannan yanki domin kare rayuku da kuma dukiyoyin mazauna arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Tun dai bayan da 'yan tawayen Seleka suka hambarar da gwamnatin Frncois Bozize ne kasar ta samu kanta cikin rikici na kabilanci da kuma addini. Duk kuma da cewa kura ta lafa bayan da aka tura rundunonin kasashen Afirka da kuma na Turai, amma kuma har yanzu ana samun sabani tsakani bangarorin da ke gaba da juna daga lokaci zuwa lokaci.