1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Mutane sun koma neman asirin bindiga

April 2, 2019

A Jihar Katsinan Najeriya jama'a da dama ne suka koma neman asirin bindiga domin kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga duk da cewa an samu wadanda aka harba suka mutu bayan sun sha maganin bindigar.

https://p.dw.com/p/3G5cj
Afrika Bildergalerie Kindersoldaten im Süd-Sudan
Hoto: DW/A. Stahl

Shan wannan maganin bindiga da wadannan al'ummomi suka kama gadan gadan abunnan ne da 'yan magana ke cewa wanda ruwa ya ci, ko takobi aka mika masa zai kama dan ceton kai. Mazauna Karamar Hukumar Batsari da ke jihar ta Katsina na a sahun gaban mutanen da suka dauki matakin shan maganin bindigar da nufin kare kai. Kuma da dama daga cikinsu sun yi imanin cewa harsashin bindigar ba zai iya ratsa su ba. Wasunsu ma sun bayar da shaida kan yadda maganin bindigar ya yi tasiri a lokuttan a lokacin da wasu maharan suka zo yankunansu amma suka rasa yadda za su yi da su. Surajo wani mazaunin Karamar Hukumar Batsari ya yi karin bayani da cewa tururuwa suke wajen shan maganin mazansu da matansu: 

"Mata suna sha da yara da kuma maza domin layi biyu ake yi akwai layin mata da yara, akwai kuma na maza. Sannan maganin idan ka sha shi cikin ikon Allah daga ka fito za ka ji babu tsoro a cikin zuciyarka gaba-daya, saboda ni na sha na ji abin da na ji a jikin nawa wallahi yana kawar da tsoro kuma maganin yana yi"
 
To sai dai daga nata bangare gwamnatin Jihar Katsina na ganin akwai hadari da kuma yaudara a game da wannan batu na asirin bindiga. A kan haka ne ta tashi tsaye wajen yin gargadi ga al'umma da ta kaurace wa ta'ammali da maganin bindigar saboda yadda ake halaka mutane da dama masu da'awar shan asirin bindigar a lokuttan hare-hare ko wata tarzoma. Dr Mustapha Mahmud Inawa shi ne sakataren gwamnatin Jihar Katsina:

Nigeria Demonstration gegen Gewalt im Bundesstaat Zamfara
Zanga-zanga akan yawan zubda jini a ZamfaraHoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba

"Mutanenmu suna da wata dabi'a da suka yarda wai suna da maganin bindiga sai ka ga da an samu wani abu sai su yunkura su bi mutanen nan cikin daji. To amma ta tabbata cewa maganin bindigar nan babu shi ba ya aiki. To kusan a yanzu duk in ka ji an yi wani kisa to irin wannan ce ta faru."

Ko kwanan nan a gundumar Wagini da ke karamar hukumar Batsari haka aka yi daga cikicin da akai kan wurin shan ruwan Dabbobi da Dankalin wani manomin akaje akai akai rigimar da mutanen nan garin suka yunkura suka bi mutanen cikin daji sukasa bindigogi suka kashe wajen mutum takwas zuwa goma kusan yanzu in kaji anyi kisa to irin wannan ne"

To sai dai duk da wannan gargadi da makunta ke yi a Jihar Katsina kan shan maganin bindigar al'ummar na ganin hakan shi kadai ne mafita wajen kare kanta daga hare-haren 'yan bindigan. Sai dai kuma ko baya ga maganin bindigar jama'a na sake komawa neman maganin karfe da duk wasu asirarai na neman kare kai. Abin da ya bude kasuwar masu maganin bindiga da kuma karfe wadanda abin asshe akasarinsu mayaudara ne kawai. Wannan ce ma ta sanya wasu mutanen ke ganin babban maganin bindiga shi ne ka tsere ka nemi mabuya kawai.

Kananan hukumomi takwas ne masu iyaka da dajin Jihar Zamfara ke fama da hare-haren 'yan bindiga a Jihar Katsina inda a yanzu kusan kowane mako sai an samu rahotan ko kashe mutane ko kuma kama su dan neman kudin fansa, lamarin da ke sanya fargaba gami da zullumi ga 'yan jihar.