1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katar na neman daidaita Kwango da Ruwanda

January 26, 2023

Katar ta nuna sha'awar shirya ganawa tsakanin shugabannin Kwango da Ruwanda don daidaita tsamin dangantakar da ke tsakaninsu. Kwango na zargin Ruwanda da goyon bayan 'yan tawaye na M23 , zargin da Ruwanda ta karyata.

https://p.dw.com/p/4Ml1D
Sarkin Katar Tamim bin Hamad Al Thani a zauren MDD da ke New York Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Ba a dai sanar da lokacin da za a yi zaman na sulhu ba, amma Katar na fatan dinke barakar da ke tsakanin Paul Kagame na Ruwanda da takwaransa na Kwango Felix Tshisekedi, bayan da bangarorin biyu suka watse baram-baram a makamancin wannan zama a watan disamban bara.

Tuni dai Kakakin fadar gwamnatin Ruwanda ya ce kasarsa a shirye take ta halarci duk wata tattaunawar wanzar da zaman lafiya da karfafa tsaro a yankinsu. Sai dai yayin da aka tuntubi mahukunta Kwango Dimokaradiya kan batun ba su ce uffan ba.

Jamhuriyar Kwango na zargin 'yan tawaye na M23 da samun goyon bayan makwabciyarta Ruwanda, yayin da ita Ruwanda ke zargin Kwangon da tallafa wa 'yan kabilar hutu domin su tada zauna tsaye a kasarsu.