1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katar ta daidata huldarta da kasar Iran

Salissou Boukari
August 24, 2017

A daidai lokacin da take tsakiyar rikicin diflomasiyya da kasar Saudiyya, kasar Katar ta sanar da daidaita gabaki dayan huldarta ta diflomasiyya tsakaninta da Iran matakin da Iran ta yaba sosai.

https://p.dw.com/p/2ilRB
Katar Doha italienischer Außenminister Angelino Alfano und Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani
Ministan harkokin wajen kasar Katar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani Hoto: picture-alliance/AA/M. Farag

Cikin wata sanarwa ce dai da ya fitar a wannan Alhamis din, ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Katar ya ce kasarsa na da burin karfafa hultarta da kasar ta Iran bayan katse huldar da suka yi bisa nuna goyon baya ga Saudiyya. Katar dai kamar Saudiyya na a karkashin jagorancin 'yan Sunni yayin da kasar ta Iran ke da mafi yawan 'yan Shi'a, ta kira jakadanta da ke kasar Iran a shekara ta 2016 bayan wani hari da wasu 'yan kasar ta Iran suka kai a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Teheran. A ranar biyar ga watan Yuni da ya gabata ne dai, kasar Saudiyya tare da kawayenta suka sanar da katse huldar diflomasiyya tsakanin su da Katar, tare kuma da daukan wasu matakai na takunkumi a kanta bisa zarginta da daurewa ta'addanci gindi, zargin da kasar ta Katar ta sha musantawa.