1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katse hanyoyin sadarwa a arewacin Najeriya

June 10, 2013

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam a kasar sun kai karar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa saboda toshe hanyoyin sadarwa a jihohin da aka kafa dokar ta baci.

https://p.dw.com/p/18nFv
African man on cellphone
Hoto: picture alliance/Anka Agency International

Wannan dai shi ne karo na farko da gamaiyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke shigar da karar gwamnatin tarayyar Najeriya da hukumar sadarwar kasar gami kamfanonin sadarwa na MTN da Airtel da Glo da Etisalat saboda toshe kafafan sadarwa a jihohin Borno, da Yobe, da kuma Adamawa wanda ke karkashin dokar ta baci, a wani mataki na yaki da jami'an tsaron Najeriya ke yi da kungiyar Boko Haram.

Tun ranar 14 ga watan Mayu ne dai al'ummomi jihohin guda uku suka wayi gari da rashin hanyoyin sadarwa na wayoyin tafi da gidanka ba tare da sanin dalilin yin hakan ba, abin da ya haifar da matsaloli gami da tsaiko a harkokin yau da kullum.
To ko menene dalilin shigar da wannan kara a daidai wannan lokaci, tambayar da na yi wa Barrister Luka Haruna ke nan babban lauyan da ya jagoranci bangaren masu shigar da kara wato Comrade Shehu Sani, da Malam Ibrahim Attahir inda ya ba ni amsa kamar haka.

This picture taken on April 30, 2013 shows a Nigerian soldier, part of the 'Operation Flush' patrolling in the remote northeast town of Baga, Borno State. Nigeria's military said on May 16, 2013 that it was ready to launch air strikes against Boko Haram Islamists as several thousand troops moved to the remote northeast to retake territory seized by the insurgents. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

"Duk da cewa dai ana samun zaman lafiya a jihohin da wannan dokar ta baci ke aiki wannan matsalar ta rashin hanyoyin sadarwa ta zama tarnaki ga harkokin kasuwanci da hadahadar kudade da kuma rashin sanin hakikanin abin da ‘yan'uwa da abokan arziki ke ciki."

Yanzu haka duk mai son sanarda ‘yan'uwansa halin da yake ciki sai ya shiga mota ya je garuruwa a jihohi makwabta wanda ba a kafa wannan doka ba abin da yake lamushe makudan kudade.

Lale maraba da matakin kai gwamnati kara

An officer of the Joint Military Task Force (JTF) patrol in the northeastern Nigerian town of Maiduguri, Borno State , on April 30, 2013. Fierce fighting between Nigerian troops and suspected Islamist insurgents, Boko Haram at Baga town in the restive northeastern Nigeria, on April 30, 2013 left dozens of people dead and scores of civilians injured. But the military denied the casualty figures claiming it was exaggerated to smear its image. Meanwhile normalcy has return to the town as residents are going about their normal business. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Al'ummomin wannan yanki da na yi sa'ar samu ta wayar tarho bayan sun fice daga yankunan sun yi marhabin da matakin na kungiyoyin kare hakkin bani Adama kamar yadda Ali Rabkana Gashua shugaban Kungiyar Muryar talaka ta Najeriya reshen jihar Yobe ya shaida min.

"Mun yi murna da wannan mataki na kungiyoyin kare hakkin bani Adama muna fata gwamnati za ta mutunta hukuncin da kotun za ta yi, ya kamata gwamnati ta duba halin da jama'a ke ciki, su sake wannan hanyoyi na sadarwa domin rayuwarmu ta dawo, mun yi murna da wannan mataki."

Sai dai Alkalin babbar kotun tarayya dake Gombe Babatunde Kadiri ya dage sauraren wannan kara har zuwa wani lokaci a nan gaba saboda ba da dama ga wadanda ake kara su bayyana a gabanta don kare kan su.

Mawallafi: Amin Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal