1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Mai sana'ar tabarmar leda

February 20, 2019

Matashi Ya'u Rufa'i Zakka wanda Gurgu ne yace ya kirkiro sana'ar ce ta yin tabarmar leda domin zama mai dogaro da kansa bayan kamma karatunsa na digiri a Jami'a.

https://p.dw.com/p/3DjfG
Global Ideas Plastikverschmutzung durch Einwegartikel
Hoto: picture-alliance/empics/K. O'Connor

Wani matashi a jihar Katsinan Najeriya da ya kammala karatunsa na jami'a ya rungumi sana'ar yin tabarmar leda. Matashin  ya ce duk da nakasar da ya ke da ita bai tsaya yin bara ko neman gwamnati ta bashi aikin yi ba, ya tashi tsaye wajen neman na kansa kuma a halin da ake ciki wannan sana'a ta rufa masa asiri har ma tuni ya fara daukar wasu matasa 'yan uwansa aiki.  

Matashin yace ya sami nassarar koyar da matasa maza da mata su kimanin 50  sana'ar ta yin tabarmar leda.

Sai dai yace yana fuskantar kalubale wajen rashin kayan aiki na zamani da kuma rashin tallafi daga gwamnati.