1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya za ta tinkari masu matsanancin ra'ayi

Suleiman BabayoApril 4, 2015

Shugaban Kenya ya yi alƙawarin ɗaukan mataki kan tsagerun masu kai hare-hare

https://p.dw.com/p/1F2lU
Kenia Garissa Universität Anschlag Trauer
Hoto: Reuters/Herman Kariuki

Shugaba Uhuru Kenyatta na ƙasar Kenya ya yi alƙawarin ɗaukan tsauraran matakai kan ƙungiyar tsagerun al-Shabaab ta ƙasar Somaliya, wadda ta kai harin da ya hallaka kimanin mutane 150 a garin Garissa na Kenya.A cikin jawabi ga al'ummar ƙasar Shugaba Kenyatta ya ce gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace sannan ya yaba wa jami'an tsaron ƙasar, inda yake cewa:

"Jami'an tsaronmu sun mayar da martani tare da hallaka huɗu daga cikin maharan, sannan aka kama biyar. Na yaba wa jami'an tsaro uku waɗanda suka rasa ransu wajen aiki wa ƙasar Kenya."Shugaban ya kara da cewa ƙasar ta Kenya za ta ci gaba da mutunta zaman tare, amma tilas a ɗauki mataki daƙile masu kaifin kishin addinin Islama da ke kai hare-hare, tare da neman haɗin kai daga shugabannin al'umma.