1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami karuwar hasarar rayuka kan ta'addanci

November 16, 2016

Yayin da aka sami raguwar hare haren ta'addanci a duniya, a waje guda kuma yawan mutanen da suka rasu sakamakon hare haren ya karu a shekarar 2015 a manyan kasashe da suka ci gaba.

https://p.dw.com/p/2Sl56
Global Terrorism Index 2016
Hoto: Institute for Economics and Peace IEP

Wani rahoto da aka fitar kan kididdigar asarar rayuka sakamakon ayyukan ta'adanci a duniya yace an sami karuwar asarar rayukan mutane a kasashen kungiyar kawancen raya ci-gaban tattalin arzikin kasashen Turai OECD da kimanin kashi 650 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Rahoton yace duk da rage kaifin tasirin kungiyar IS da kuma Boko Haram da sojojin suka yi a cikin gida sun haddasa hasarar rayuka da dama a kasashen ketare. 

Rahoton ya kara da cewa a duniya baki daya an sami asarar rayukan mutane dubu 29 da 376 a sakamakon ayyukan ta'addanci a shekarar da ta gabata, sai dai kuma an sami raguwar kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka gabata. Kasashen Denmark da Faransa da Jamus da Sweden da kuma Turkiya su ne a kan gaba a nahiyar Turai wajen fuskantar yawaitar asarar rayuka a sakamakon ayyukan ta'addanci cikin shekara guda tun bayan shekara ta 2000 a cewar rahoton. 

Kashi 72 cikin dari na asarar rayukan an same su ne a kasashen Iraqi da Afghanistan da Najeriya da Pakistan da kuma Siriya da ke zama kasashe biyar na kan gaba a jadawalin asarar rayukan a duniya. Yayin da Amirka ta ke a matsayi na 36, Faransa ta 29, Rasha a matsayi na 30 sai kuma Birtaniya wadda ke a matsayi na 34. Hare-haren ta'addanci ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasashe inda aka yi asara ta kimanin sama da dala biliyan 89.